Hadiman Buhari na take dokar zirga-zirga tsakanin jihohi - Fadar shugaban kasa

Hadiman Buhari na take dokar zirga-zirga tsakanin jihohi - Fadar shugaban kasa

Mataimaki na musamman ga shugaban kasa a kan harkokin yada labarai, Garba Shehu, ya ce wasu daga cikin hadiman shugaban kasa na zirga-zirga tsakanin jihohi duk da hanawar da gwamnati da hukumar yaki da cututtuka masu yaduwa (NCDC) suka yi.

A yayin zantawa da gidan talabijin din Channels a ranar Litinin, Shehu ya ce ana barin zirga-zirga tsakanin jihohi matukar mutum ya bada dalili mai karfi.

Shehu ya yi martani ne a kan rikicin dan uwan Buhari, Sabiu Yusuf wanda aka fi sani da Tunde wanda ya ki killace kansa bayan tafiyar da yayi zuwa Legas.

Shehu ya ce, "Fadar shugaban kasa bata gaza ba. A duk lokacin da matafiyi ya nuna ya matsu, ana barinsa. Ko a fadar shugaban kasar ba a yini guda ba tare da samun bako daga wata jihar ba.

Hadiman Buhari ya take dokar zirga-zirga tsakanin jihohi - Fadar shugaban kasa
Hadiman Buhari ya take dokar zirga-zirga tsakanin jihohi - Fadar shugaban kasa Hoto: The Cable
Asali: UGC

"Abinda ba a so shine yawo mara tushe. Idan har mutum ya bayar da dalili mai gamsarwa, to jami'an tsaro na barinsa zuwa inda suke so. A tunanina hakan na faruwa a duk fadin kasar nan."

A lokacin da aka kalubalance shi kan batun cewa jama'a masu aiki na musamman ne kadai aka yarda su je wata jiha, Shehu ya jaddada cewa jama'a ne ke daukar kayayyaki daga wuri zuwa wuri.

"Muna bin dokar NCDC da ma'aikatar lafiya. Banbancin fadar shugaban kasa da sauran wurare shine kowa yana kallon kowa," yace.

A lokacin da aka tambayi Shehu ko Tunde zai koma aiki a yau, Shehu ya ce, "Idan ya so, zai zo. Ba zan yi mamaki dan bai je ba kuma ba zan yi mamaki ba idan ya je."

KU KARANTA KUMA: COVID-19: Tsabar yunwa ta sa mu fashi da makami - Matasa masu fashi

A makon da ya gabata ne 'yan sanda suka damke hadiman Aisha Buhari shida bayan rikicin da tayi da Tunde.

Sai dai, Aisha Buhari ta bukaci babban sifeton rundunar 'yan sanda (IGP), Mohammed Adamu, ya saki jami'an tsaron da ke bata kariya.

A cikin kwanakin nan ne Tunde ya dawo daga tafiya kuma an yi ikirarin cewa ya hadu da mai cutar korona.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng