Edo 2020: PDP na tsaka mai wuya a kan Obaseki

Edo 2020: PDP na tsaka mai wuya a kan Obaseki

A kokarin gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki na komawa jam'iyyar PDP don samun tikitin takarar kujerar gwamnan a zaben 19 ga watan Satumba da ke karasowa, jam'iyyar ta fada tsaka mai wuya.

A makon da ya gabata ne jam'iyyar APC ta hana Obaseki tsayawa takara karkashin inuwarta.

A yayin bayani game da abinda yasa aka hana Obaseki tsayawa takara, Dr. Abubakar Fari ya ce:

"Obaseki ya ce ya kammala digirinsa a jami'ar Ibadan a 1976 amma shaidar da ya hada a fom dinsa ta nuna 1979 wanda hakan ya ci karo."

Ya kara da cewa, gwamnan na da katin zabe biyu mabanbanta wanda hakan ba bisa ka'ida bane.

Edo 2020: PDP na tsaka mai wuya a kan Obaseki
Edo 2020: PDP na tsaka mai wuya a kan Obaseki Hoto: Vanguard
Asali: UGC

Kwamitin ya ce ya samu rashin daidaito a fom din da Obaseki ya kawo.

An rufe siyar da fam din PDP a ranar 2 ga watan Yuni tare da kammala tantancewa a ranar 5 ga watan Yuni. Mutum uku aka tantance lafiya kalau a halin yanzu.

Kamar yadda jam'iyyar ta bayyana a daren jiya, wadanda aka tantance kadai ne za su fito zaben fidda gwani. Don haka Obaseki ba zai iya fitowa ba.

Za a yi zaben fidda gwani na jam'iyyar PDP a ranar Juma'a. Amma kuma INEC ta bukaci a mika 'yan takara kafin ranar 13 ga watan Yuli.

"Gaskiya PDP ta manta da Obaseki ko kuma ta shirya rungumar hukunci sakamakon ayyukanta," wani lauya yace.

Wata majiya ta PDP ta ce: “Muna a tsaka mai wuya kuma jam’iyyarmu na fuskantar gwaji na amana. Obaseki na kokarin neman hanyar shiga ta kowani hali da kuma mallakar tikitin takarar gwamna a PDP.

“Wannan gwamna ne da bai sanar da sauya shekarsa zuwa PDP ba. Mafita guda da ya rage shine neman dukka yan takarar su janye masa ko kuma a bari ayi zaben fidda gwani sannan a bukaci wanda ya yi nasara ya janye masa.

KU KARANTA KUMA: Tsaro: APC ta yi wa PDP raddi a kan bukatar murabus din Masari

Amma shin za mu yi adalci ga dukkanin yan takararmu, musamman wanda ya lashe zaben fidda gwani?

“Kuma Obaseki na kokarin ganin ya ci gaba tare da mataimakinsa, Phillip Shaibu a matsayin abokin takararta.”

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel