Shugaban kasa da Gwamnoni ba su ga damar kawo zaman lafiya ba ne – Junaid Mohammed

Shugaban kasa da Gwamnoni ba su ga damar kawo zaman lafiya ba ne – Junaid Mohammed

Sanatan jamhuriyya ta biyu, Junaid Muhammed ya marawa kungiyar Dattawan Arewa watau NEF baya a game da zargin da ta ke yi na cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari da gwamnonin Arewa sun gaza shawo kan matsalar tsaro.

Dr. Junaid Muhammed ya yi hira da jaridar Vanguard a waya a karshen makon da ya gabata, ya ce an san fuskokin miyagun da su ke kashe jama’a, amma ba a yi wani abu a game da lamarin ba.

A tattaunawar, Junaid Muhammed ya ce: “Duk wanda ke da nauyin tsare jama’a ya gaza. Kuma babu wanda zai iya cewa ga wanda ke kokarin kare rai da dukiyar mutane. Ko shugaban kasa ne ko gwamnoni ko kuma wasu da ke rike da mukamai a bangaren tsaro.”

Dattijon ya ce halin da ake ciki ya kai ace abin ya na da ban tsoro domin kasar ta zama babu wani tsari.

“Na biyu shi ne akwai wata alaka tsakanin masu tada kafar baya da kuma wasu manya a Arewa, shiyasa babu wanda ya ke yi wa wadannan miyagu wani abu duk da cewa an san fuskarsu.”

Mohammed ya zargi gwamnati da shirga karyayyaki a game da halin da ake ciki a kasar. A cewarsa, sai yadda ‘yan bindiga su ka yi da mutanen yankin Arewa a wannan lokaci da ake ciki.

KU KARANTA: Abin da ya jawo ake fama da rashin tsaro a kasa - PDP

Shugaban kasa da Gwamnoni ba su ga damar kawo zaman lafiya ba ne – Junaid Mohammed
Dr. Junaid Mohammed
Asali: Facebook

“A cikin makon da ya wuce an kai hari a Arewa maso gabas kusan sau uku ko hudu idan zan iya tunawa. Kuma miyagu sun aukawa Zamfara da jihar Shugaban kasa, don haka babu wanda zai fito ya yi mana jawabi, ya na cewa ana samun nasara.”

“Hakika babu tsaro kuma abin da Dattawan Arewa su ka fada game da ‘yan bindiga gaskiya ne. Maganar gaskiya, rashin ganin dama ne ya hana ko shugaban kasa da Gwamnoni su yi maganin ‘yan bindiga.”

“Miyagun ‘yan bindigan nan sanannu ne, kuma su na dangantaka da wasu mutane masu daraja.” Mohammed ya kara da cewa: “Shugaban kasa ko gwamnoni su yi abin da doka ta da ce. A kai (wadanda aka kama) kotu.”

"Na tuna lokacin gwamnatin Zamfara ta ce ta samu wasu Sarakuna da laifin hada-kai da ‘yan bindiga, aka kama su kuma gwamnan ya ce zai gurfanar da su a kotu. Wani tsohon Janar din soja ya nema masu alfarma aka sake su.”

“Idan kana da wani tsohon Soja ko ‘dan siyasa a bayanka, duk abin da ka yi, za ka sha.”

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel