Fallasa: Shugaban jam'iyya na zargin kokarin tube Magu daga kujerarsa

Fallasa: Shugaban jam'iyya na zargin kokarin tube Magu daga kujerarsa

- Dan Nwanyanwu, shugaban jam’iyyar ZLP ya yi zargin cewa ana shirin tsige Magu daga kujerarsa

- Ya ce wasu yan siyasa da ke da laifin hamdame kudade ne ke wannan kulla-kullan

- Nwanyanwu ya ce sun hada kai domin cimma manufar tasu don kada a binciki munanan ayyukan tasu

- Jigon siyasan ya ce sun hada kudade don cimma hakan

Shugaban jam'iyyar Zenith Labour Party (ZLP), Dan Nwanyanwu ya zargi wasu 'yan siyasa da shirin cire Magu daga shugabancin hukumar yaki da rashawa tare da yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa daga kujerarsa.

Nwanyanwu ya sanar da manema labarai hakan ne a garin Abuja. Ya zargi wasu tsoffin gwamnoni da 'yan siyasa da ake bincika a kan handamar kudin kasa da kokarin ganin saukar Magu.

Shugaban Hukumar EFCC; Ibrahim Magu
Shugaban Hukumar EFCC; Ibrahim Magu Hoto: Vanguard
Asali: UGC

Ya ce: "Bayanan sirrin da ya iske mu ya nuna cewa wasu 'yan siyasa sun hada kansu tare don sauke Ibrahim Mustapha Magu daga kujerarsa.

"Wadannan mutane sun hada da tsoffin shugabanni a kasar nan da yake bincika. Sun hada manyan kudade don janye hankalin wasu sassa na gwamnati da ke da kusanci da shugaban kasa.

"Kokarinsu shine ganin bayan wanda ke jagorantar yaki da almundahanarsu. Suna son ganin an cire shi da gaggawa daga kan kujerarsa.

KU KARANTA KUMA: COVID-19: Yaki da korona na hannunku - El-Rufai ga jama'ar Kaduna

"Wasu daga cikinsu na gaban kotu yayin da wasu ba a zo kansu ba. Amma basu son hakan ta faru. Wannan ne yasa suka hada kawunansu tare da hada makuden kudade don janye hankali."

A wani labari na daban, mun ji cewa wani sashe na jam'iyyar APC ta bukaci a kori Gwamna Godwin Obaseki da wasu mutum biyu na jam'iyyar sakamakon zargin su da ake da al'amuran zagon kasa ga jam'iyya.

Bangaren ya bukaci kwamitin ayyuka na kasa karkashin jagorancin Oshiomhole da ya sallami Obaseki wanda cikin kwanakin nan aka haramtawa fitowa takara.

Bangaren da ya samu jagorancin Kanal David Imuse ya sanar da manema labarai a ranar Lahadi cewa ba za su amince da ayyukan zagon kasa ga jam'iyyar ba.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel