Boko Haram sun hallaka mutane 35 a kananan hukumomi 2 a Jihar Borno
- ‘Yan ta’addan Boko Haram sun kai wasu hare-hare a Nganzai da Munguno
- An kashe mutane akalla 35 a wadannan Garuruwa a karshen makon jiya
- Boko Haram sun kona ofishin ‘Yan Sanda da wani ofishi na majalisar UN
Rahotanni sun ce ‘yan ta’addan Boko Haram sun kashe akalla mutane 35, yayin da su ka jikkata mutane da-dama a lokacin da su ka kai hari a wasu kananan hukumomi biyu a jihar Borno.
Mabambantan majiyoyi sun tabbatar da cewa ‘yan ta’addan sun kai hari a Nganzai da Munguno, inda su ka far ma kananan yara da mata. ‘Yan ta’addan sun kuma kona gidajen Bayin Allah.
Haka zalika mayakan na Boko Haram sun yi gaba da kayan amfanin gona daga garuruwan.
A ranar Lahadi, wani mutumi ya shaidawa jaridar Daily Trust cewa mayakan Boko Haram sun auko masu ne da kimanin karfe 10:00 na safe, su ka kuma kashe yara da mata kimanin 35.
Sojojin Boko Haram sun kai hari a wani ofishin ‘yan sanda har su ka saki mutane, sannan kuma su ka kona ofishin. Bayan haka ‘yan kungiyar ta’addan sun kai hari a wani ofishi na UN.
KU KARANTA: An kashe mutane a wani hari da aka kai a Jihar Benuwai
A wannan karamin ofishi na majalisar dinkin Duniya, an bankawa wasu motoci uku wuta.
Legit.ng Hausa ta yi magana da wani mazaunin yankin a lokacin da abin ya faru, inda ya tabbatar da cewa babu shakka an kai hari a wadannan kananan hukumomi na Munguno da Nganzai.
Wani Bawan Allah da ke zama a yankin ya ce jami’an tsaro su na bakin kokarinsu, sai dai ‘yan ta’addan su kan yaudari jama’a har su kai ga samun nasara wajen hallaka su cikin ruwan sanyi.
Wannan munanan hare-hare sun auku ne kwanaki kadan bayan an kashe mutane a wani kauye a karamar hukumar Gubio. A Gubio, Boko haram sun yi gaba da mai garin, da wasu mutum biyar.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng