Farfesa Shehu Modibbo ya koka a kan halin da ake ciki yau a Yankin Arewa

Farfesa Shehu Modibbo ya koka a kan halin da ake ciki yau a Yankin Arewa

Wani farfesa kuma jagoran jam’iyyar APC a jihar Kaduna, Shehu Usman Modibbo, ya ce Arewacin Najeriya na fama da kalubale iri-iri a karkashin gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari.

Shehu Usman Modibbo wanda ‘dan gani kashe-nin shugaban kasa Muhammadu Buhari ne a jihar Kaduna, ya bayyana wannan ne ya na cikin kuka da hawaye a wani bidiyo da ya bayyana.

A wannan bidiyo da ya fito, Modibbo wanda aka fi sani da Danfulani, ya koka akan halin da mutanen Arewacin Najeriya da yankin ya shiga.

Farfesa Shehu Modibbo ya yi magana ne a harshen Hausa, ya na mai takaicin matsayin cigaban da Arewa ta samu kanta. Wannan bidiyo ya shiga hannun PRNigeria ne a ranar Asabar.

Tsohon kwamishinan na gwamnatin Nasir El-Rufai, ya ce a daidai lokacin da sauran yankuna su ke ganin ayyukan gwamnati, Arewacin Najeriya sun buge ne da ruba-ruban kwangiloli ko kuma su ka tashi a tutar babu a wasu wurare a yankin.

“Tituna a wasu bangarorin kasar sun yi nisa ko kuma an kammala su. Amma wadanda ke Arewa, an yi watsi da su. Kuma har ya gama mulkinsa, manyan titunan da ke Arewa irinsu hanyar Kano zuwa Abuja da sauransu ba za su kammalu ba.”

KU KARANTA: Gwamnan APC ya ba barbadawa masoya kasa a ido, ya ce ya gama takara

Ya ce: “Hanyoyin Arewa sun kara ragargajewa. Idan ana maganar titin dogo, har yau batun titin jirgin kasar Kano zuwa Abuja ta Kaduna sai dai a mafarki, babu abin da aka yi. Babu maganar wanda su ka yi alkawari daga Kano zuwa Katsina har Daura.”

Kamar yadda rahotanni su ka bayyana, farfesan ya yi wannan jawabi ne ya na hawaye, ya ce mutanen Najeriya sun zabi Muhammadu Buhari ne saboda mutunci da darajarsa, da kuma aikin da ya faro a 2015.

Amma ganin yadda ake fama da rashin tsaro a irinsu Zamfara, Sokoto, Katsina, da Kaduna, Modibbo ya ce noma ba zai yiwu a wadannan wurare ba.

Ya kara da cewa: “Saboda haka ina kira gare ka, shugaban kasa Muhammadu Buhari ka kawo mana dauki.”

'Dan siyasar ya rufe jawabin na sa da cewa: “Ka kawowa wadanda su ka zabe ka agaji. Don mun zabe ka, ba zai hana mu fada maka gaskiya mai daci a lokacin da abubuwa su ka daina tafiya daidai ba.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel