Siyasa Edo: Sai bayan Gwamna Obaseki ya zauna da Buhari zai yi magana

Siyasa Edo: Sai bayan Gwamna Obaseki ya zauna da Buhari zai yi magana

Gwamna Godwin Obaseki na jihar Edo, ya ce zai fadi mataki na gaba da zai dauka bayan ya zauna da shugaban kasa Muhammadu Buhari bayan an hana shi neman tikiti a karkashin jam’iyyar APC.

Godwin Obaseki wanda ya ke neman tazarce a jam’iyyar APC ya gamu da matsala ne bayan da kwamitin tantance masu neman takara ta haramtawa gwamnan na jihar Edo neman tikiti a APC.

Gwamna Obaseki ya yi wannan jawabi ne a dandalin Twitter a ranar Lahadi, 14 ga watan Yuni, 2020.

Gwaman ya ce: “Na ji dadin goyon baya da ana-tare da mutanen jihar Edo da ‘Yan Najeriya su ka nuna mani a sakamakon zaluncin da kwamitin tantance ‘yan takara na jam’iyyar APC ta yi mani.”

KU KARANTA:

“Zan sanar da matakin gaban da zan dauka bayan na gama tattaunawa da magoya baya na da shugaban kasa Muhammadu Buhari.” Inji sa.

Jonathan Ayuba wanda shi ne shugaban kwamitin tantance ‘yan takara ya haramtawa Obaseki ne saboda kura-kurai da aka samu a takardun satifiket dinsa.

Kafin yanzu gwamnan na jihar Edo ya yi jawabi a game da halin da ake ciki a game da annobar COVID-19 wanda ta kashe mutane 25 a cikin watanni uku.

Yanzu haka jiga-jigan jam’iyyar PDP su na kokarin ganin sun karkatar da hankalin Godwin Obaseki. Daga ciki har da Atiku Abubakar da Nyesom Wike.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel