Ya kamata Gwamnati ta yi maganin ‘Yan bindiga ne ba ƙwari ba - Kwamred Sani

Ya kamata Gwamnati ta yi maganin ‘Yan bindiga ne ba ƙwari ba - Kwamred Sani

- Shehu Sani ba ya goyon bayan a kashe Biliyoyi wajen kashe ƙwarin gona

- Gwamnatin Tarayya ta na da shirin yaƙi da ƙwarin da ake addabar gona

- ‘Dan siyasar ya ce abin da ya fi dacewa shi ne ayi maganin ‘Yan bindiga

Yayin da gwamnatin tarayyar Najeriya ta bayyana cewa za ta kashe Naira biliyan 13 wajen yaƙi da ƙwarin gona a jihohi 12, wasu sun fito sun soki wannan mataki.

Daga cikin wadanda su ka yi tir da wannan shawara akwai tsohon sanata, Shehu Sani, wanda ya fito ya nuna adawarsa ga wannan makudan biliyoyin da za a kashe.

Sanata Shehu Sani ya ba gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari shawarar cewa ta yi maganin miyagun ‘yan bindigan da su ke addabar Bayin Allah a jihohin kasar.

Shehu Sani ya ce idan har aka kashe ‘yan ta’adda da su ke hallaka mutane a Najeriya, jama’a za su tashi da kansu su tafi gonaki, kuma su yi maganin ƙwari su yi noma.

KU KARANTA: Sojoji sun yi fada da Jami'an Kwamitin yaki da COVID-19 a Borno

Ga abin da Shehu Sani ya rubuta a shafinsa Twitter: “Da farko, ku kashe miyagun ‘yan bindiga da ‘yan ta’adda ta yadda mutane za su je gonaki su kashe ƙwarin gonar.”

‘Dan siyasar da ya taba wakiltar Kaduna ta tsakiya a majalisar dattawa ya kara da cewa: “Ta ya za ku kashe dodannin gona, ku ƙyale dodannin da ke riƙe da makamai?”

Sani ya yi wannan bayani ne a yau Lahadi, 14 ga watan Yuni, 2020 da kimanin karfe 9:00 na safe.

Wasu su na ganin wannan shiri da gwamnati ta ke yi ba shi ne ya dace a yanzu ba, ganin irin ta’adin da ‘yan bindiga su ke yi, wanda zai iya kawowa harkar noma cikas.

Kafin yanzu kuma Sanatan ya yabi shugaba Buhari da ya martaba gwagwarmayar marigayi MKO Abiola, amma ya ce duk a banza idan ana kashe mutane a fadin kasar.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel