Zamfara: Sojoji sun lalata sansanin Dogo Gide, sansanin da ya gagari shiguwa tun 2013

Zamfara: Sojoji sun lalata sansanin Dogo Gide, sansanin da ya gagari shiguwa tun 2013

Dakarun soji sun lalata sansanin gagararren shugaban kungiyar 'yan bindiga, Dogo Gide, yayin wani hari da rundunar soji ta kai ranar Lahadi, 7 ga watan Yuni.

Sojoji sun kai harin ne a daidai lokacin da Dogo da saura abokansa da yaransa ke kara mike kafafu tare da kara fadin sansanin da suka kafa tun shekarar 2013.

Jaridar HumAngle ta rawaito cewa Dogo da Kachalla Yellow, wani shugaban 'yan bindiga, ne suka fara kafa sansanin a 'Birni' bayan sun tashi jama'ar kauyen da ake kira 'Birni' a shekarar 2013.

"Babu wani mahaluki da zai iya zuwa sansanin a kafa," a cewar majiyar HumAngle yayin tattaunawa da wakilin jaridar.

"Ana kiran wurin Kango, kuma yana karkashin karamar hukumar Maru, wacce ke arewa da dajin Kuyanbana a jihar Zamfara.

"Tunaninsu shine su kafa wani sansani da zasu zauna tare da iyalinsu sannan su ajiye makamansu. Burinsu shine su cigaba da fadada sansanin a hankali.

"Sansanin ya zama gida ga 'yan bindiga daga wurare na kusa da nesa da suka hada Jamhuriyar Nijar, Katsina, Kogi, Neja Kaduna da Sokoto.

"Nan suke zuwa su buya tare da tsara yadda zasu cigaba da kai hare - hare. Zai daukesu lokaci mai tsawo kafin su sake gina wani sansanin mai girmansa," a cewar majiyar.

Zamfara: Sojoji sun lalata sansanin Dogo Gide, sansanin da ya gagari shiguwa tun 2003
Zamfara: Sojoji sun lalata sansanin Dogo Gide, sansanin da ya gagari shiguwa tun 2003
Asali: UGC

Manjo janar John Enenche, jagoran watsa labaran atisayen rundunar soji na kasa, ya ce an kai harin ne a karkashin atisayen 'ACCORD'.

Enenche ya bayyana cewa dakarun soji sun kai harin ne bayan samun sahihan bayanan sirri da kuma leken asiri da na'urori da suka tabbatar da cewa akwai gine - ginen da 'yan bindigar ke boye cikinsu a cikin surkukin dajin.

DUBA WANNAN: 'Masana'anta ce' - Ahmed Lawan ya fadi sirruka a kan kungiyar Boko Haram

HumAngle ta rawaito cewa Dogo Gide tare da wasu tsirarun shugabannin 'yan bindigar sun tsira da raunukan harbin bindiga yayin harin, kuma yanzu haka suna samun kulawa a asibitin Dandallah da ke yankin karamar hukumar Maru.

Wasu daga cikin mutanen da aka tserar daga hannun 'yan bindigar sun tabbatar da cewa an kashe daruruwan 'yan ta'adda.

Daga cikin kwamandojin da suka lissafa cewa an kashe akwai Yellow, Daqi da Shadi.

Rundunar soji ta kai harin ne ta hanyar amfani da jiragen yaki masu aman wuta. Sojoji sun saki bama - bamai a kan sansanin, kamar yadda mutanen da aka kubutar suka sanar.

Mutanen sun bayyana cewa sun yi nasarar tsallake rijiya da baya sakamakon ajiyesu da 'yan bindigar suka yi a wani wuri nesa da sansaninsu.

Dakarun soji sun kama dumbin makamai da 'yan bindigar suka boye a dajin.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel