Harin Monguno: An kashe sojoji 20, farar hula 40, an kona ofishin 'yan sanda

Harin Monguno: An kashe sojoji 20, farar hula 40, an kona ofishin 'yan sanda

Wani farar hula da ke taimakon rundunar tsaro a yaki da 'yan ta'adda ya sanar da cewa mayakan kungiyar Boko Haram sun kashe a kalla sojoji 20, farar hula 40 tare da raunata wasu da dama yayin wasu tagwayen hare - hare da suka kai a jihar Borno.

Tagwayen hare - haren da aka kai a Monguno da Nganzai na zuwa ne a cikin 'yan kwanaki kalilan bayan mayakan kungiyar Boko Haram sun kai wani mummunan hari tare da kashe mutane 81 a yankin Gubio.

Wasu ma'aikatan kungiyoyin jin kai da mazauna yankin sun shaidawa kamfanin dillancin na 'Reuters' cewa mayakan kungiyar Boko Haram dauke da mugayen makamai da motocin yaki sun dira a Monguno da misalin karfe karfe 11:00 na safiyar ranar Asabar.

Mayakan sun nunawa jami'an tsaron gwamnati fin karfi, inda suka kashe a kalla sojoji 20 tare da shafe kusan sa'a uku suna cin karensu babu babbaka a garin.

Majiyar ta sanar da cewa an raunata daruruwan fararen hula yayin musayar wuta tsakanin mayakan kungiyar Boko Haram da dakarun rundunar soji.

Kafafen yada labarai sun rawaito cewa asibitin garin Monguno ya cika makil da mutanen da aka raunata, lamarin da ya tilasta wasu kwanciya a wajen asibitin suna jiran samun taimako daga wurin ma'aikatan lafiya.

Mayakan kungiyar Boko Haram sun lalata sansanonin kungiyoyin jin kai na kasa da kasa tare da kone ofishin rundunar 'yan sanda a Monguno.

Harin Monguno: An kashe sojoji 20, farar hula 40, an kona ofishin 'yan sanda
Tawagar Sojoji
Asali: Facebook

Kazalika, sun rabawa mazauna yankin wata wasika a cikin harsshen Hausa, inda a ciki suka gargadesu a kan su guji yin aiki da sojoji da kungiyoyin jin kai na kasashen ketare.

DUBA WANNAN: 'Masana'anta ce' - Ahmed Lawan ya fadi sirruka a kan kungiyar Boko Haram

Bayan Mongunzo, mayakan Boko Haram sun shiga Nganzai a ranar Asabar, inda suka kashe farar hula dan sa kai (CJTF), kamar yadda mazauna yankin suka sanar.

Wani mazaunin yankin ya bayyana cewa mayakan sun dira Nganzai a cikin motoci da babura, kuma sun kashe fararen hula fiye da 40.

Aljazeera ta rawaito cewa kakakin rundunar soji bai amsa kira domin yin magana a kan harin ba. Kazalika, ba a samu wani ma'aikacin majalisar dinkin duniya (UN) da zai magana a kan harin ba.

Kungiyar ISWAP ta dauki alhakin kai harin na ranar Asabar da kuma wanda aka kai Gubio a makon da ya gabata.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel