Buhari ya alakanta kullen COVID-19 da yawaitar ta'addanci a Katsina da Borno

Buhari ya alakanta kullen COVID-19 da yawaitar ta'addanci a Katsina da Borno

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya danganta kashe-kashen 'yan bindiga da kuma na mayakan Boko Haram da dokar kullen da aka saka a kasar nan sakamakon annobar Coronavirus.

Shugaban kasar wanda ya bayyana hakan yayin jawabi ga 'yan Najeriya a ranar Damokaradiyya, ya nuna damuwarsa a kan yadda rayukan jama'a ke salwanta sakamakon al'amuran 'yan ta'adda a fadin kasar nan.

Kamar yadda yace, gwamnatin sa ta fifita kawo karshen duk wani nau'i na rashin gaskiya kuma dakarun sojin kasar nan sun murkushesu, Daily Nigerian ta ruwaito.

Buhari ya alakanta kullen COVID-19 da yawaitar ta'addanci a Katsina da Borno
Buhari ya alakanta kullen COVID-19 da yawaitar ta'addanci a Katsina da Borno Hoto: Premium Times
Asali: UGC

Ya ce: "Dukkan kananan hukumomi da mayakan suka kwace a Borno, Yobe da Adamawa duk an kwato su sannan mazauna yankin sun dawo gidajensu.

"Ina matukar damuwa a kan mummunan rashin da jihohin Katsina da Borno ke yi a cikin kwanakin nan.

"'Yan ta'addan na yin amfani da annoba ne da ta hana mutane walwala wurin aiwatar da miyagun ayyuka. Jami'an tsaro za su damko masu laifin tare da tabbatar da adalci.

KU KARANTA KUMA: Rashin tsaro: Shugabannin NASS za su yi taro da Buhari

"Dole ne in yi kira ga mazauna jihar da kananan hukumomi da su bada bayanan sirri ga jami'an tsaro a yayin da suka ji labarin za a kai musu hari.

"Ina mika ta'aziyyata ga dukkan 'yan uwa da yankunan da abun ya shafa."

A gefe guda, mun ji cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce ‘yan Najeriya na fuskantar wahala sosai sakamakon annobar Coronavirus.

Ya fadi hakan ne a jawabinsa na ranar yancin kai a ranar Juma’a, 12 ga watan Yuni, jaridar The Punch ta ruwaito.

Ya ce: “Rana ce ta karrama magabatanmu wadanda suka yi wahala wajen samar da jumhuriyyarmu da duk wani dan Najeriya da ya yi aiki ba ji ba gani domin dorewar ta.

“Muna bikin damokradiyyar wannan shekarar duk da annobar coronavirus wacce ta raunana kasarmu da duniya baki daya.

“Shakka babu wannan lokaci ya kasance mawuyaci ga kowa, musamman wadanda suka rasa masoya sakamakon cutar. Da kuma wadanda suka rasa hanyoyin rike kansu sakamakon tsatsauran matakin da muka shimfida a kowani mataki na gwamnati domin magance annobar da tsare rayuka."

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel