Har gobe ni uban gidan Rauf Aregbesola ne a APC – inji Bola Tinubu

Har gobe ni uban gidan Rauf Aregbesola ne a APC – inji Bola Tinubu

A ranar Talata ne Jagoran jam’iyyar APC mai mulki, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya fito ya yi watsi da rade-radin da ke yawo na cewa akwai sabani tsakaninsa da Minista Rauf Aregbesola.

Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa har gobe shi mai gidan Rauf Aregbesola ne. Bola Tinubu ya yi wannan magana ne ta bakin hadiminsa, Tunde Rahman.

Ga abin da jigon na APC ya ke fada a jawabinsa: “Babu rikici ko wata rigima ta bayyane ko ta karkashin kasa tsakaninmu (Tinubu da Ogbeni Rauf Aregbesola)."

Bola Tinubu ya na cikin manyan wadanda su ka yi sanadiyyar da Rauf Aregbesola ya zama abin da ya zama a siyasar Najeriya, bayan ya zakulo sa a lokacin da ya ke gwamna.

A farkon makon nan ne hukumar dillacin labarai ta rahoto cewa yaran tsohon gwamnan na Legas sun ruguza duk wata kungiyar siyasa da ke karkashin jam’iyyar APC.

Bayan kungiyar GAC wanda ita ce tamkar majalisar kolin siyasar APC a Legas ta wargaza duk wata kungiyar siyasa, wasu sun fara tunanin cewa an samu baraka a gidan Bola Tinubu.

KU KARANTA: Tinubu ne ya taimaka mani a siyasa - Tsohon Gwamnan Osun

Har gobe ni uban gidan Rauf Aregbesola ne a APC – inji Bola Tinubu
Bola Tinubu Hoto: Facebook
Asali: Depositphotos

Fitaccen ‘dan siyasar ya ce ba a taba samun lokacin da shi da tsohon gwamnan jihar Osun, Aregbesola, su ka samu sabani ba.

“A yau majalisar da ke ba gwamna shawara, babbar kungiyar da ke zartar da hukunci a jam’iyyar APC a Legas ta dauki matakin wargaza duk wasu kungiyoyin taware da ke cikin jam’iyyar.”

“An yi wannan ne domin a samu karin tarbiya da hadin-kai da zaman lafiya, tare da tabbatar da shugabancin jam’iyya. APC gida daya ce a Legas. Ina nan a matsayin mai gidan Ogbeni Aregbesola.” Inji Tinubu.

Ya ce: “Mu na nan da karfinmu. GAC ta na da karfi a cikin jam’iyyar APC na reshen jihar Legas.”

‘Dan siyasar ya ce babu wanda ake hari a matakin da GAC ta dauka, sai dai don kurum a kara dankon zumunci. Tinubu ya ce ka da wani ya yi mummunar fassara ga matsayar da aka cin ma.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel