El-Rufai ya haramta fita, ya ce kowa ya zauna a gida a inda rikici ya barke

El-Rufai ya haramta fita, ya ce kowa ya zauna a gida a inda rikici ya barke

- Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya sanya takunkumin fita a wasu kananan hukumomi biyu

- Hakan ya biyo bayan barkewar rikici a yankunan saboda wani gona

- Dokar kullen zai shafe sa’o’i 24 ne kuma ya fara aiki ne a nan take

- Kwamishinan tsaron cikin gida na jihar, Samuel Aruwan ne ya fitar da sanarwar

Gwamnatin jihar Kaduna ta saka dokar kulle na sa’o’ i 24 a yankin Atyap na karamar hukumar Zangon Kataf da Chawai da ke karamar hukumar Kauru.

A bisa ga wata takarda da gwamnatin jihar ta wallafa a shafinta na twitter daga kwamishinan tsaron cikin gida na jihar, Samue Aruwan, ya ce dokar hana fitan zai fara aiki ne a nan take.

El-Rufai ya haramta fita, ya ce kowa ya zauna a gida a inda rikici ya barke
El-Rufai ya haramta fita, ya ce kowa ya zauna a gida a inda rikici ya barke Hoto: Thisdaylive
Asali: UGC

A yanzu haka jami’ an tsaro na kokarin kwantar da tarzoman da ya taso daga wani rikici da ya barke a makon da yagabata kan wani gona a Zangon-Kataf, wanda shugabannin yankin suka yi kokarin sasantawa amma sai ya zarta tunani.

Samuel Aruwan da kwamishinan yan sandan jihar ma suna yankin, inda suke jagorantar kokarin da ake na dawo da zaman lafiya.

Jawabin ya zo kamar haka: “Gwamnatin jihar Kaduna ta sanar da sanya dokar hana fita na sa’o’i 24 a yankin Atyap da ke karamar hukumar Zangon Kataf da Chawai a karamar hukumar Kauru.

“Wannan dokar kulle na sa’o’i 24 zai fara aiki a nan take.

“Hukumomin tsaro na kwantar da tashin hankalin da ke tasowa daga wani rikici a makon da ya gabata kan wani gona a Zangon Kataf wanda shugabannin yankin suka yi kokarin sasantawa amma sai ya ci tura.”

A wani labarin kuma, mun ji cewa mummunan hargitsi a tsakanin kabilun Lafia da ke iyakar jihohin Adamawa da Gombe ya kashe rayukan jama'a masu tarin yawa.

An kashe jama'a masu tarin yawa tare da halaka dabbobi da kuma salwantar dukiyoyi.

Lafiya gari ne da ke karamar hukumar Lamurde a jihar Adamawa.

An gano cewa rikicin ya barke ne sakamakon fada a kan gonaki.

Mataimakin gwamnan jihar, Crowther Seth ya ziyarci yankin inda ya samu rakiyar Birgediya kwamandan Yola, Birgediya Janar Sani Gambo Mohammed da sauran shugabannin tsaro.

Mataimakin gwamnan ya tabbatar da cewa gwamnati za ta bankado wadanda suka yi aika-aikar. Ya kara da jan kunnen masu assasa rigimar.

KU KARANTA KUMA: Boko Haram: Rundunar soji ta ragargaza 'yan ta'addan suna tsaka da taro

Rundunar 'yan sandan jihar a jiya ta ce ta damke mutum 32 da ake zargi da hannu cikin rigimar.

Tuni aka rufe wasu kananan hukumomi biyu a kan rikicin kabilancin.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel