Korona: Gwamnan Abia ya bayyana halin da yake ciki a cibiyar killacewa
- Gwamnan jihar Abia, Okezie Ikpeazu ya ce yana samun sauki sosai a cibiyar killace masu cutar korona
- Ikpeazu ya kuma bayar da tabbacin cewa zai dawo nan ba da jimawa ba domin ci gaba da sauke hakkin da ya rataya a wuyansa na shugabancin jama'a
- A ranar Litinin ne kwamishinan yada labarai na jihar Abia, ya sanar da cewa Ikpeazu ya kamu da cutar korona kuma an killacesa tun bayan fitar sakamakon
Gwamna Okezie Ikpeazu na jihar Abia ya ce yana samun sauki a cibiyar killacewa bayan kamuwa da yayi da cutar korona.
Enyinnaya Apollos, mai magana da yawun gwamnan ya sanar da hakan yayin zantawa da shi a ranar Laraba, 10 ga watan Yuni.
Gwamnan ya kara da kira ga tawagarsa da su ci gaba da shugabancin jihar yadda ya dace yayinda yake sa ran dawowa bada jimawa ba.
A wallafar da yayi a shafinsa na Facebook, Apollo ya ce: "Ikpeazu ya tabbatar da cewa yana samun lafiya kuma babu dadewa zai dawo."
A ranar Litinin, John Okiyi Kalu, kwamishinan yada labarai na jihar Abia, ya sanar da cewa Ikpeazu ya kamu da cutar korona kuma an killacesa tun bayan fitar sakamakon.
Ya ce gwamnan ya umarci mataimakinsa da ya ci gaba da tafiyar da al'amuran jihar har zuwa lokacin da zai dawo.
A halin yanzu, jihar Abia na da mutum 97 da suka kamu da cutar korona.
KU KARANTA KUMA: Harkallar filaye: Kotu ta yi watsi da karar tubabben Sarki Sanusi
A wani labarin na daban, mun ji a baya cewa wani ma'aikacin gidan gwamnatin jihar Gombe ya rasu sakamakon annobar korona, lamarin da yasa aka rufe ofishin sakataren gwamnatin jihar tare da bada umarnin yin feshi a asibitin gidan.
Shuaibu Danlami darakta ne na ayyuka na musamman da siyasa a ofishin sakataren gwamnatin jihar kuma ya rasu a ranar Lahadi bayan gajeriyar rashin lafiya, kwamitin yaki da annobar korona ta jihar ta sanar.
An diba samfur dinsa wanda sakamakon ya bayyana cewa yana dauke da cutar korona a ranar Talata, shugaban kwamitin, Idris Mohammed ya sanar a ranar Laraba.
Ya ce ofishin sakataren gwamnatin da gidan gwamnatin duk za a kulle su don yin feshi tare da daukar samfur din dukkan ma'aikatan don gwaji.
Danlami mamba ne kuma mataimakin sakataren kwamitin yaki da cutar na jihar kuma an dauka samfur din dukkan 'yan kwamitin.
Danlami ne mutum na bakwai da ya rasu sakamakon annobar korona a jihar Gombe.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng