Makarantun Gwamnati za su koma karatu a Ranar 16 ga watan Yuni - Ayade

Makarantun Gwamnati za su koma karatu a Ranar 16 ga watan Yuni - Ayade

Duk wasu makarantun gwamnatin jihar Kuros Riba za su koma bakin aiki a ranar 16 ga watan Yuni, 2020. Gwamnatin jihar ta shirya matakai domin kare dalibai da kuma sauran ma’aikata.

A halin yanzu Kuros Riba ce kurum jihar da babu mutum ko guda mai fama da cutar Coronavirus a fadin Najeriya. Gwamnatin jihar za ta yi bakin kokarinta na ganin cewa wannan ya daure.

Mai girma gwamna Ben Ayade ne ya bada sanarwar bude makarantun boko da ke jihar.

Gwamna Ben Ayade ya yi wannan jawabi ne ta bakin hadimin da ke taimaka masa wajen hulda da jama’a da yada labarai watau Mista Christian Ita a ranar Laraba, 10 ga watan Yuni, 2020.

Christian Ita ya ce gwamnan ya yi wannan jawabi ne a lokacin da ya kaddamar da wasu daga cikin kayan PPE da masakar gwamnatin Kuros Riba ta hada domin yaki da cutar COVID-19.

Gwamnatin Ayade ta fara hada kayan kariya na PPE da za ayi amfani da su yayin da aka koma aji a makarantun jihar. Za a jarraba yiwuwar cigaba da karatu a lokacin wannan annoba.

KU KARANTA: Ba zan hana mutane zirga-zirga saboda COVID-19 ba inji Gwamna Ben Ayade

Makarantun Gwamnati za su koma karatu a Ranar 16 ga watan Yuni - Ayade
Ben Ayade Hoto: Wikipedia
Asali: Facebook

Mai magana da yawun bakin gwamnan ya ce daga cikin kayan kariyar da ake hadawa akwai tukunkumin rufe fuska da dogayen riguna da za a rabawa malaman asibiti da ‘yan makaranta.

Gwamnatin Ben Ayade za ta rabawa mutanenta wadannan kaya ne kyauta ba tare da an biya sisin kobo ba. Gwamnan ya nuna cewa jihar za ta nemi hanyar da za ta cigaba da zama da cutar.

“Ina tunanin ya kamata yaranmu su koma makaranta, na ga an yi wannan a kasar Sin, inda yara su ke zuwa karatu da takunkumin rufe fuska da hanci.” inji gwamnan jihar ta bakin kakakinsa.

“A Kuros Riba yaranmu ba za su cigaba da zama a gida ba, iyakar zamansu a gida, iyakar sangarcewar da za su yi da tabarbarewar tarbiyya da kuma lalacin da za su samu.” Inji sa.

Ayade ya ce idan an je makaranta sai a cire takunkumin hanci a bar na fuska saboda numfashi.

Tun a ranar 19 ga watan Maris ne gwamnatin Najeriya ta bada umarnin rufe duka makarantu.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel