“A wace Jami’ar ka je ka yi karatu?” – Obaseki ya dura kan Oshiomhole

“A wace Jami’ar ka je ka yi karatu?” – Obaseki ya dura kan Oshiomhole

Gwamna Godwin Obaseki na jihar Edo ya kalubalanci shugaban jam’iyyar APC na kasa, Adams Oshiomhole, ya fadawa Duniya jami’ar da ya je ya yi karatunsa na Digiri.

An shigar da gwamna Godwin Obaseki kotu, inda ake zarginsa da badakalar shaidar digiri.

Masu karar su na zargin cewa gwamnan na APC ya na amfani da takardun bogi ne da ke nuna cewa ya yi Digiri a jami’ar Ibadan. A dalilin haka masu wannan zargi su ka roki kotu ta haramta masa takarar gwamnan jihar Edo da za ayi a watan Satumban nan mai zuwa.

Adams Oshiomhole ya kaddamar da kwamitocin da za su tantance ‘yan takara kuma su saurari korafi a zaben fitar da gwanin jam’iyyar APC a jihar Edo, inda ya bukaci wannan kwamiti su binciki zargin da ke kan wuyan gwamna mai-ci watau Mista Godwin Obaseki.

Oshiomhole ya ce: “Wani ya tafi jami’ar UI (Ta Ibadan) ya raba wannan gardama, a bar tada maganar. Idan satifiket din Obaseki na gaskiya ne, ya aka yi ya tsallake matakin tantancewa a lokacin baya?

Na san cewa a wancan lokaci da wannan mutumi bai taba mafarkin zai yi gwamna ba, a kan tantance kowane dalibi ko daga wani gida ka fito, kafin ka shiga jami’a.” inji shugaban na APC.

KU KARANTA: Obaseki ya fara karaya daga zaben Edo tun kafin tafiya ta yi nisa

Da gwamnan ya ke maida martani, ya yi kaca-kaca da shugaban jam’iyyar ta sa. Gwamnan na Edo ya jefawa Oshiomhole kalubalen ya bayyana sunan jami’ar da ya yi karatunsa.

Obaseki ya maida martani ne ta bakin mai magana da yawunsa, Crusoe Osagie wanda ya fadawa jaridar Punch cewa Adams Oshiomhole ya fito ya fadi makarantar da ya je ya yi Digiri.

Crusoe Osagie ya wanke mai gaidansa, ya ce: “Jami’ar UI kusan ta na cikin makarantun da ta fi kowace daraja a Afrika, ita ta ba Obaseki shaidar Digirin B.A tun a 1979. Jami’ar ta na nan.”

Ya ce: “Duk wanda bai yarda da satifiket din ba, me zai hana shi ya je makarantar ya tabbatar? Meyasa sai a kafafen yada labarai kawai mu ke jin wannan.”

Osagie ya sake cewa babu gaskiya a zargin domin Godwin Obaseki ya na cikin tsofaffin daliban Jami'ar UI da aka zaba su ka gabatar da lacca a 2018.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng