Kada ku bar rayukan jama'a ta su tafi a haka - Buhari ga dakarun soji

Kada ku bar rayukan jama'a ta su tafi a haka - Buhari ga dakarun soji

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi kira ga dakarun sojin kasar nan da kada su saurarawa 'yan Boko Haram. Ya ce su fanshe rayukan jama'arsa da aka kashe a kauyen Faduma Kolomdi da ke karamar hukumar Gubio da ke jihar Borno.

Jaridar The Cable ta ruwaito yadda aka kashe mutum 80 sakamakon harin 'yan Boko Haram a ranar Talata.

A wata takarda da Malam Garba Shehu ya fitar, mai magana da yawun shugaban kasar ya ce Buhari ya matukar firgita da wannan kisan gillar.

Shugaban kasar ya kwatanta al'amarin da abun takaicin da ya faru ana saura kwanaki kadan zagayowar ranar damokaradiyya.

Buhari ya yi kira ga sojin Najeriya da su tabbatar da nasara a kan 'yan ta'addan.

Ya ce, "Wannan harin na daya daga cikin miyagun hare-haren da aka kai wa jama'a a yankin arewa masu gabas.

"Buhari ya matukar firgita a kan al'amarin barnar da 'yan Boko Haram suka yi a kauyen Faduma da ke Borno."

"Shugaban kasar na tsammanin bayani dalla-dalla daga Gwamna Farfesa Babagana Zulum a kan ziyarar da ya kai wa yankin.

"A yayin kushe al'amarin, shugaba Buhari ya bukaci sojin Najeriya da su tabbatar da nasara a kan 'yan ta'addan ta hanyar kawo karshensu tare da kwato duk jama'ar da suka yi garkuwa da su tare da Shanu.

"Ya mika ta'aziyyarsa ga gwamnati da jama'ar Najeriya da yankin baki daya."

Kada ku bar rayukan jama'a ta su tafi a haka - Buhari ga dakarun soji
Kada ku bar rayukan jama'a ta su tafi a haka - Buhari ga dakarun soji. Hoto daga The Cable
Asali: Twitter

KU KARANTA: Yanzu-yanzu: Majalisa ta musanta umartar EFCC da ta binciki ministan Buhari

A ziyarar da Zulum ya kai wa kauyen, daya daga cikin wadanda suka ga yadda 'yan Boko Haram suka halaka jama'a a kauyen Faduma Kolomdi da ke karamar hukumar Gubio ta jihar Borno a ranar Talata, ya bada labarin yadda aka yaudaresu.

Mutumin, wanda ya tattauna da Gwamna Babagana Umara Zulum na jihar yayin da ya ziyarci kauyen a ranar Laraba, ya ce an kashe mutane 81 tare da illata mutum 13 da kuma yin garkuwa da wasu bakwai.

"Mayakan ta'addancin sun iso a motocin yaki wurin karfe 10 na safe. Sun kwashe sa'o'i shida suna ruwan wuta don sai karfe 4 na yamma suka bar kauyen," yace.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel