Shugabannin Jam’iyyar APC sun dakatar da Sanata Bulkachuwa a Jihar Bauchi

Shugabannin Jam’iyyar APC sun dakatar da Sanata Bulkachuwa a Jihar Bauchi

- APC ta dakatar da Sanata Muhammad Adamu Bulkachuwa a Jihar Bauchi

- Shugabannin APC sun ce ba a sake ganin Sanatan tun da ya tafi Majalisa ba

- Jam’iyyar APC ta ce Sanatan ba ya zuwa jaje ko ya yi wa jama’a wani aiki

Jam’iyyar APC ta reshen jihar Bauchi, ta dakatar da sanata mai wakiltar Bauchi ta Arewa, Muhammad Adamu Bulkachuwa a dalilin kusufin da ya yi wa al’ummarsa.

Rahotanni sun bayyana cewa an dakatar da sabon sanatan na Jam’iyyar APC ne saboda watsi da mutanensa da ya yi tun bayan da aka rantsar da shi a majalisar tarayyar kasar.

Shugabannin APC na Kafin Kuka, a mazabar Kofar Gabas da ke karamar hukumar Katagum a jihar Bauchi su ka sanar da wannan mataki da aka dauka a yau ranar Talata.

Shugaban APC na mazabar, Sa’adu Muhammed ya shaidawa ‘yan jarida a ofishin jam’iyyar APC cewa sanatan ya kauracewa mutanen mazabarsa da kuma ‘ya ‘yan jam’iyya.

KU KARANTA: Yadda za ka rika samun labaran Legit.ng Hausa a shafinka da zarar an wallafa

Shugabannin Jam’iyyar APC sun dakatar da Sanata Bulkachuwa a Jihar Bauchi
Sanata Muhammad Adamu Bulkachuwa
Asali: UGC

Sa’adu Muhammed ya fadawa manema labarai cewa sanatan bai leko gida ko domin ya yi wa jama’a jajen annobar Coronavirus da ta’aziyyar mace-macen da aka rika yi ba.

“Mutanen yankin Katagum sun shiga wani halin ban-tausayi na takaici da haushi da tsananin bukata a dalilin halin sanatan wanda ya yi watsi da su.” Inji Alhaji Muhammed.

“Sanata Bulkachuwa ya bace a Duniya, ya yi watsi da mazabarsa na fiye da watanni shida, babu wani gagarumin aiki da za a zo a gani a mazabarsa duk tsawon wannan lokaci.”

Sanata Muhammad Adamu Bulkachuwa mai shekaru 80 a Duniya ya lashe zaben majalisar dattawa ne a 2019. Kusan wannan ne karonsa na farko da ya shiga siyasa sosai.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel