NERC ta tsayar da ranar hana yanke wutar lantarkin marasa mita

NERC ta tsayar da ranar hana yanke wutar lantarkin marasa mita

- NERC, hukumar gwamnatin tarayya mai kula da harkokin da suka shafi hasken wutar lantarki, ta ce ya zama dole a daina yanke wutar 'yan Najeriya marasa mita

- Hukumar ta umarci DISCOs su rabawa kwastomominsu mita domin cajinsu adadin wutar da suka yi amfani da ita a wata

- A cewar NERC, DISCOs zasu iya yanke wutar gidan duk wanda ya ki amincewa a saka masa sabuwar mitar

Hukumar kula da harkokin da suka shafi hasken wutar lantarki a kasa (NERC) ta sanar da shirinta na tilasta fara amfani da matakin da ta dauka na hana yanke wutar kwastomomi marasa mitar lantarki ta zamani.

Tilasta aiki da matakin zai shafi kamfanonin raba hasken wutar lantarki (DISCOs) guda bakwai wadanda har yanzu suka ki yin biyayya ga umarnin NERC mai lamba 197/2020 a kan a daina yanke wutar kwastomomin da basu da mita.

NERC ta bayyana shirinta na tilastawa kamfanonin a cikin wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na Tuwita (@NERCNG) ranar Talata.

NERC ta tsayar da ranar hana yanke wutar lantarkin marasa mita
Mitar wuta
Asali: Twitter

A cewar NERC, DISCOs da hukuncin zai shafa sun hada da wadanda suke Benin, Enugu, Eko, IKeja, Kano, Kaduna da Fatakwal.

DUBA WANNAN: Rabon tallafin annobar korona: Matawalle ya caccaki minista Sadiya Farouk

NERC ta bawa DISCOs din wa'adin kwana 14, daga ranar 4 ga watan Yuni, a kan su aiko cikakken bayanin dalilin da yasa ba za a ci tararsu ba, saboda kin yin biyayya ga umarnin hukuma.

A umarnin da NERC ta bawa DISCOs, ta umarcesu a kan su daina yanke wutar duk kwastoman da basu bawa mitar da ke auna adadin wutar da ya ke amfani da ita ba.

Kazalika, NERC ta umarci DISCOs su yanke wutar duk wanda aka bawa mita amma ya ki amincewa ya yi amfani da ita.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel