Oshiomhole bai yarda a soke tallafin fetur a Gwamnatin Obasanjo ba – Inji Atiku
Atiku Abubakar, wanda tsohon mataimakin shugaban kasa ne a Najeriya ya ce Adams Oshiomhole, shugaban jam’iyyar APC mai-ci, bai goyi bayan cire tallafin man fetur da aka yi a lokacin Olusegun Obasanjo ya na mulki ba.
A wani bayani a shafin sadarwa na twitter, Atiku wanda ya yi wa Obasanjo mataimaki tsakanin shekarar 1999 zuwa 2007 ya ce shi ne wanda aka daurawa alhakin zama ya tattauna da shugaban kungiyar ta NLC, amma aka yi ta kawo masa matsala.
“Gwamnatin Obasanjo wanda na yi wa aiki ta dauki matakin cire tallafin man fetur. Ni aka daurawa nauyin tattaunawa domin ayi sulhu da shugaban kungiyar a wancan lokaci kuma shugaban jam’iyyar APC na yanzu, wanda ya nuna bakar adawa.”
Ko da Atiku Abubakar bai kama sunan kowa ba, sanannan abu ne cewa a wancan lokaci Adams Oshiomhole ne shugaban kungiyar kwadago ta kasa watau NLC.
Alhaji Atiku Abubakar ya ce adawar da kungiyar kwadagon da Adams Oshiomhole ya ke jagoranta ba ta sa gwamnatin tarayya ta fasa cire gaba daya tallafin mai a kasar ba.
KU KARANTA: Yadda za ka rika samun labaran Legit.ng Hausa a shafinka da zarar an wallafa
“Duk da haka, mun yi nasarar daukar matakai biyu wajen zare tallafin man fetur da bakin mai kafin mu bar ofis.”
Atiku Abubakar da Olusegun Obasanjo sun bar gwamnati ne a 2007, inda Ummaru Musa ‘Yar’adua ya karbi mulki.
Cire tallafin man fetur ya na nufin mai zai kara tsada a fadin kasar, wanda hakan ya jawo Oshiomhole ya jagoranci ‘yan kwadago su ka shiryawa gwamnatin PDP zanga-zanga.
Obasanjo a wancan lokaci ya ce gwamnati ba za ta iya cigaba da kashe kusan Dala biliyan 1 wajen ragewa ‘yan kasa farashin fetur ba, ya yi alkawarin kashe kudin wajen wasu muhimman abubuwa.
Sai kuma ga shi yanzu gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta APC da hukumar PPPRA ta sanar da irin wannan mataki, tare da cire farashin da aka yi wa man fetur, Atiku ya goyi bayan wannan matsaya.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng