Mun buƙaci a sake yi wa Orji Uzor Kalu sabuwar shari’a a kotu – Lauyan EFCC

Mun buƙaci a sake yi wa Orji Uzor Kalu sabuwar shari’a a kotu – Lauyan EFCC

- Hukumar EFCC ta ce za ta kuma komawa kotu da Sanata Orji Uzor Kalu

- Orji Uzor Kalu ya fito daga gidan yari ne bayan wani hukuncin kotun ƙoli

Hukumar EFCC mai yaƙi da masu yi wa tattalin arziƙin Najeriya zagon ƙasa ta ce ta na jiran babban Alƙalin kotun tarayya ya sake miƙawa wani Alƙali shari’ar Orji Uzor Kalu.

EFCC ta na buƙatar ayi wa tsohon gwamnan na jihar Abia sabuwar shari’a ne kamar yadda kotun ƙoli ta zartar. Babban lauyan hukumar EFCC, Rotimi Jacobs ya bayyana wannan.

A ranar Talata, 9 ga watan Yuni, 2020, Rotimi Jacobs ya shaidawa jaridar Punch cewa EFCC ta gabatar da takarda gaban kotu, inda ta ke neman a sake gabatar da wannan shari’a.

Rotimi Jacobs SAN ya ce yanzu za su jira a sanar da Alƙalin da zai saurari sabuwar shari’ar da za a sake yi tsakanin EFCC da sanata Orji Uzor Kalu wanda ya fito daga gidan kurkuku.

A Disamban 2019 ne kotu ta samu Orji Uzor Kalu da laifin wawurar Naira biliyan 7.1 daga baitul-malin gwamnatin jihar Abia, a dalilin haka Alƙali ya yanke masa ɗaurin shekara 12.

KU KARANTA: Yadda za ka rika samun labaran Legit.ng Hausa a shafinka da zarar an wallafa

Mun buƙaci a sake yi wa Orji Uzor Kalu sabuwar shari’a a kotu – Lauyan EFCC
Orji Uzor Kalu Hoto: NgrSenate
Asali: UGC

Sai dai kuma daga baya kotun ƙoli ta yi fatali da wannan hukunci, inda ta ce Alƙali mai shari’a Mohammed Idris bai da hurumin da zai saurari wannan shari’a bayan ya bar kotun.

A sakamakon haka ne babban kotun Najeriya ta ce dole a nemi sabon Alƙali da zai saurari shari’ar. An shafe shekaru 12 kafin yanzu ana faman wannan shari’a ta EFCC da Kalu.

Rotimi Jacobs ya ke cewa: “Ba za mu daɗa wasu ƙarin ƙara ba. Mun buƙaci CJ (Alƙalin Alƙalai) ya sake ba wani sabon Alƙali shari’ar kamar yadda Alƙalin kotun ƙoli ya yanke hukunci.

Babban Lauyan na gwamnatin ya ce: “Ba mu samu labarin ko an ba wani Alƙalin shari’ar ba."

A shari’ar da EFCC ta yi nasara a kan tsohon gwamnan, an zargi Orji Uzor Kalu da laifuffuka 34. Daga ciki akwai amfani da wani kamfanin iyalinsa wajen sace dukiyar jihar Abia.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel