Zanga - zanga ta barke a Katsina

Zanga - zanga ta barke a Katsina

A ranar Talata ne mazauna garin Yantumaki a karamar hukumar Danmusa a jihar Katsina suka yi tururuwar fitowa kan tituna domin gudanar da zanga - zanga a kan halin rashin tsaro da suke fama da shi.

Zanga - zangar ta barke ne sakamakon sace wani ma'aikacin lafiya da diyarsa da wasu 'yan bindiga suka yi.

Wata majiya ta shaidawa jaridar Premium Times cewa wasu 'yan bindiga ne suka kaiwa ma'aikacin lafiyar, Mansir Yusuf, hari da misalin karfe 1:00 na dare tare da yin awon gaba da shi da diyarsa.

Garkuwa da ma'aikacin lafiyar da diyarsa na zuwa ne a cikin kasa da mako biyu da kai hari tare da kashe hakimin Yantumaki, Atiku Abubakar, wanda 'yan bindiga suka harbe a gidansa.

Wata majiya da ta nemi a boye sunanta ta sanar da Premium Times cewa ma'aikacin lafiyar da aka sace makwabci ne ga hakimin da 'yan bindiga suka kashe.

Zanga - zanga ta barke a Katsina
Ma su zanga - zanga a Katsina Hoto: Premium Times
Asali: UGC

Masu zanga - zangar, yawancinsu matasa da kananan yara, sun rufe manyan hanyoyi, tare da caccakar gwamnati a kan nuna halin 'ko in kula' tun bayan kisan hakimin garin.

Ma su zanga - zangar sun lalata tare da kone wani allon yakin neman zaben shugaban kasa, Muhammadu Buhari, da gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari.

Zanga - zanga ta barke a Katsina
Ma su zanga - zanga na kone allon kamfen din Buhari da Masari
Asali: Twitter

"Har yanzu babu wani jami'in tsaro a garin tun bayan kisan hakimi. Mu na yin zanga - zanga ne domin jan hankalin gwamnati kafin wadannan 'yan bindigar su fara kawo mana hari kowacce rana.

DUBA WANNAN: Sojoji sun lalata sansanin shugaban 'yan bindiga, Dan Jangeru, sun kashe wasu, sun kama wasu (Hotuna)

"Sun kashe hakimin garinmu, yanzu sun kara dawowa. Hakan na nufin zasu cigaba da dawowa kenan tunda basa fuskantar wani kalubale duk lokacin da suka kawo hari. Ya kamata gwamnati ta dauki matakin da ya dace kafin al'amura su gama lalacewa," a cewar wani jagora a garin Yantumaki.

DSP Gambo Isah, kakakin rundunar 'yan sandan jihar Katsina, bai amsa kiran Premium Times domin jin ta bakin rundunar 'yan sanda ba.

Karamar hukumar Danmusa ta jihar Katsina ta yi iyaka da karamar hukumar Zurmi da ke jihar Zamfara.

Jihohin Katsina, Sokoto da Zamfara na fuskantar yawaitar hare - haren 'yan bindiga a 'yan kwanakin baya bayan nan.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel