Shahararren mai garkuwa da mutane, Wadume, ya gurfana gaban kotu

Shahararren mai garkuwa da mutane, Wadume, ya gurfana gaban kotu

Hamisu Bala, mutumin da ake zargi da kasancewa mashahurin mai garkuwa da mutane ya gurfana a gaban wata babbar kotun tarayya da ke Abuja a kan zarginsa da ake da laifin ta'addanci.

Yunkurin kama Wadume ya janyo rasa rayukan 'yan sanda uku tare da dan farar hula daya a jihar Taraba. Amma kuma 'yan sanda sun damke Wadume a watan Augusta na shekarar 2019.

A watan Fabrairu da ya gabata, sifeta janar din 'yan sanda ya mika laifuka 16 gaban kotu da ake zargin Wadume da su wadanda suka hada da ta'addanci.

Amma kuma ofishin Antoni janar din tarayya ya karba gabatar da karar. An rage zargin zuwa 12 daga 16 na farko.

An sake rage wadanda ake zargin daga 20 zuwa mutane 7.

Shahararren mai garkuwa da mutane, Wadume, ya gurfana gaban kotu
Shahararren mai garkuwa da mutane, Wadume, ya gurfana gaban kotu Hoo: The Cable
Asali: UGC

Ana zargin Wadume da wadannan laifukan ne tare da Aliyu Dadje (Sifetan dan sanda), Auwalu Bala wanda aka fi sani da omo razor, Uba Bala wanda aka fi sani da Uba Delu, Bashir Waziri wanda aka fi sani da Baba runs.

Sai kuma Zubairu Abdullahi wanda aka fi sani da Basho da kuma Rayyanu Abdul.

Dukkan wadanda ake zargin sun ki amsa laifuka 12 da ake zargin su da shi da suka hada da "ta'addanci, garkuwa da mutane, ci gaba da tsarewa da kuma karbar miliyan 106."

Lauyan Wadume T. Dangana, ya sanar da kotu cewa har yanzu ba a ce komai ba a kan bukatar belin da ya mika gaban kotu ba kuma wanda yake karewa na farko yana fama da matsanancin rashin lafiya don ko tari yayi, jini ke fita daga bakinsa.

Shuaibu Lawan, babban lauya daga ma'aikatar shari'a, ya ce ba za a duba bukatar belin ba don ta dogara ne a kan laifukan farko.

KU KARANTA KUMA: Sabon tsarin Facebook: Yadda zaka rika ganin labaran Legit.ng Hausa a shafinka da dumi-dumi

"Bukatar na da madogara da zargi na farko da aka mika gaban kotun amma ba a kan wadannan ba. Amma muna maraba da sabuwar bukata kuma za mu dubata yadda ya dace," yace.

Duk da haka, ya ce babu bukatar da za ta dakatar da sauraron shari'ar amma za a gaggauta.

A hukuncin alkalin kotun Binta Nyako, ta bada umarnin ci gaba da tsare wadanda ake zargin.

Ta kara da bada umarnin cewa a bar masu kare kansun su ga lauyoyinsu a yayin da suke tsare tare da basu tallafi game da lafiyarsu a asibitin 'yan sanda. Ta bukaci bayanin likita game da ingancin lafiyar mutum na farko da ake kara.

"A kawo min rahoton lafiyarsa. Idan akwai bukata, zan bada umarnin kai shi babbar asibiti," tace.

An dage sauraron karar zuwa ranar 22 ga watan Yunin 2020.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel