Gwamnan APC da shugaban jam'iyyar sun saka fadar shugaban kasa a tsaka mai wuya

Gwamnan APC da shugaban jam'iyyar sun saka fadar shugaban kasa a tsaka mai wuya

- Ana ci gaba da cece-kuce a kan tsarin zaben fidda gwani na jam'iyyar APC a zaben gwamnan Edo

- Kwamitin zartarwa na jam'iyyar APC ya aminta da salon kato bayan kato inda bangaren Obaseki ke son wakilan jam'iyyar su fito don yin zaben

- An gano cewa fadar shugaban kasar ta shiga halin tsaka mai wuya a kan wannan al'amari

Yanayin zaben fidda gwanin dan takarar gwamnan APC na jihar Edo har yanzu ba a tsayar ba kuma yana ci gaba da kawo cece-kuce.

Zuwa yanzu ba a san zaben fidda gwanin da za a yi a ranar 22 ga watan Yuni ba.

A yayin da kwamitin zartarwa na jam'iyyar APC ya aminta da salon kato bayan kato, inda duk mai shaidar zama dan jam'iyya zai iya yin zaben fidda gwanin.

Magoya bayan Gwamna Godwin Obaseki ba su aminta da wannan ba. Sun fi son wakilan jam'iyyar su fito don yin zaben.

Gwamnan APC da shugaban jam'iyyar sun saka fadar shugaban kasa a tsaka mai wuya
Gwamnan APC da shugaban jam'iyyar sun saka fadar shugaban kasa a tsaka mai wuya Hoto: TVC
Asali: Twitter

Gwamnan na ta rokon fadar shugaban kasa da ta soke hukuncin kwamitin zartarwar jam'iyyar.

KU KARANTA KUMA: Sabon tsarin Facebook: Yadda zaka rika ganin labaran Legit.ng Hausa a shafinka da dumi-dumi

An gano cewa fadar shugaban kasar ta shiga halin tsaka mai wuya a kan wannan al'amari.

Wannan barakar a kan yanayin zaben fidda gwanin ya kai ga kotu inda bangaren shugaban jam'iyyar na kasa, Adams Oshiomhole ke tsananta yakin neman kada Obaseki.

'Yan takara biyar ne ke adawa da Obaseki su ne: Pius Odubu, Osagie Ize-Iyamu, Chris Ogiemwonyi, Matthew Iduoriyekemwen da Osabo Obazee.

Shugaban jam'iyyar APC na Edo ta tsakiya, Chief Francis Inegbeniki, wanda yake na hannun daman Adams Oshiomhole, ya tattara laifuka 50 na Obaseki wadanda sun isa su hana gwamnan zarcewa.

Ya ce da yawa daga cikin 'yan jam'iyyar ba su amince da Obaseki da mataimakinsa ba saboda rashin jituwar da ke tsakaninsa da shugaban jam'iyyar tare da manyan jiga-jigan jam'iyyar.

KU KARANTA KUMA: COVID-19: 'Yan Najeriya miliyan 20 ne za su iya rasa aikinsu

Wata majiya ta ce, bangaren gwamnan na ta kokari tare da bibiyar duk wadanda fadar shugaban kasa za ta ji don hana zaben kato bayan kato.

Har yanzu mabiya bayan gwamnan na hango hatsari a zaben kato bayan kato, wanda suka ce ba za a iya kiyaye dokar nesa-nesa da juna ba don dakile annobar korona.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel