COVID-19: 'Yan Najeriya miliyan 20 ne za su iya rasa aikinsu

COVID-19: 'Yan Najeriya miliyan 20 ne za su iya rasa aikinsu

Shugaban majalisar dattijai, Sanata Ahmed Lawan ya ce idan annobar COVID-19 ta ci gaba, a kalla 'yan Najeriya miliyan 20 ne za su iya rasa aikinsu.

Lawan ya kara da cewa, siyasar kasa da kasa ke hana Najeriya samar da makaman zamani don amfanin rundunar soji wajen fatattakar rashin tsaro.

A yayin jawabi ga manema labarai a garin Abuja yayin shirye-shiryen bikin zagayowar shekara na majalisar, Lawan ya ce duk lokacin da Najeriya ta bukaci siyan makamai daga kasashen ketare, ana daukar tsawon lokaci kafin aminta da hakan.

COVID-19: 'Yan Najeriya miliyan 20 ne za su rasa aikinsu
COVID-19: 'Yan Najeriya miliyan 20 ne za su rasa aikinsu Hoto: Premium Times
Asali: UGC

Ya ce: "A gaskiya muna fama da siyasar kasa da kasa. A wani kokarin siyan sassan jiragen sama da muka yi, mun kwashe watanni shida kafin su amince. Amma wata kasa bata wuce watanni biyu take samu.

KU KARANTA KUMA: Sabon tsarin Facebook: Yadda zaka rika ganin labaran Legit.ng Hausa a shafinka da dumi-dumi

"A gaskiya ba daidai bane amma za mu iya cewa wannan ne babban kalubalen da muke fuskanta."

A yayin bayyana halin da kasar nan take ciki a fannin tsaro, ya ce akwai bukatar daukar tsauraran matakai a kan hakan.

"Ba mu da isassun kayan aiki na jami'an tsaro. Gwamnati na iya bakin kokarinta wajen samar da kayayyakin bukata," yace.

Ya jaddada bukatar hadin kai tsakanin mahukunta da masu zartar da doka. Ya ce rashin hadin kan da ke tsakaninsu ne yasa ake fuskantar kalubale mai tarin yawa.

A bangaren caccakarsu da ake a kan bashin da za a karbo wa kasar nan, Lawan ya ce sun aminta da cin bashin ne don tabbatar da an ci gaba da ayyukan kayan more rayuwa wanda gwamnatin tarayyar bata da kudin ci gaba da aikin.

KU KARANTA KUMA: Wallahi albashina bai wuce mun kwana 10 yake karewa – Gudaji Kazaure

Ya ce, "muna bukatar $14.2 biliyan don aiwatar da ayyukan kasafin kudin 2020 sakamakon zuwan annobar korona da illolinta.

"Ba mu yi amfani da damar mu ba lokacin da ya kamata. Ba mu fadada tattalin arziki mu ba ko saka hannayen jari a bangarorin da ya kamata ba.

"A yanzu lokaci yayi da za mu shawo kan matsalar rashin ababen more rayuwa. Akwai ayyuka kamar na gada ta biyu ta Niger, wutar lantarki ta Mambila, titin jiragen kasa na Legas zuwa Kano amma bamu da kudi."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel