Gwamnatin Tarayya za ta sa haraji a kan irinsu Facebook da Netflix

Gwamnatin Tarayya za ta sa haraji a kan irinsu Facebook da Netflix

- Gwamnatin Najeriya za ta rika karbar haraji a kan wasu kamfanonin waje

- Irinsu Facebook da Twitter za su rika biyan haraji na kudin da su ka samu

- Wadannan kamfanoni su na samun kudi a Najeriya ta hanyar talla da bidiyo

A ranar Litimin, 8 ga watan Yuni, 2020 aka fitar da rahoto cewa ana kokarin sa haraji ga kamfanonin sada zumunta da yanar gizo da su ke aiki, su na samun kudi da Najeriya.

Gwamnatin tarayya Najeriya za ta shigo da haraji ne kan kamfanoni da ke da shafukan wallafa bidiyo, da na kallo da kuma masu dandalin sada zumunta da ke yin kudi da ‘yan kasar.

A shekarar nan ne Ministar tattalin arziki, Zainab Ahmed ta kawo wata dokar haraji wanda ta yi wa dokar kudi ta 2019 garambawul domin Najeriya ta samu damar tatsar kamfanonin.

Ministar kudin ta kawo wannan doka ne da nufin daurawa wadannan kamfanoni na zamani haraji na abin da su ka samu, za a rika biyan wannan haraji ne ga hukumar FIRS.

KU KARANTA: Yadda za ka rika samun labaran Legit.ng Hausa a shafinka da zarar an wallafa

Gwamnatin Tarayya za ta sa haraji a kan irinsu Facebook da Netflix
Ministar kudi Hoto: Facebook/Zainab Shamsuna Ahmed
Asali: Instagram

Netflix, Facebook, da Twitter, su na cikin kamfanonin waje da su ke da shafukan wallafa bidiyo da na kallo da kuma tallata hajjoji a Najeriya, hakan na nufin su na samun kudi a kasar.

Sauran kamfanoni irinsu Alibaba da kuma Amazon su na samun kudi a Najeriya ne ta hanyar karbar bayanai wurin ‘yan kasar domin shigo masu da kayan da su ka saya daga ketare.

Jaridar Punch ta ce wannan dokar da aka kawo za ta yi aiki ne kan duk wani kamfanin ketare da ya ke samun kudin shiga na akalla Naira miliyan 25 a Najeriya a cikin shekara guda.

Sannan kuma gwamnati za ta rika karbar haraji a kan kamfanonin da ke amfani da shafukan yanar gizo masu ajin (.ng). Za a rika karbar wannan haraji ne sau guda duk shekara.

Rahoton ya ce za a saukake wannan doka a kan kudin da aka samu da ‘yan kasar wajen da ke zaune a Najeriya, da kuma hidimar da aka yi ga hukumomi da kuma makarantun ilmi.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel