Oshiomhole ya na fada da Obaseki ne saboda ya ki sakin kudi – Inji Idahosa
Tsohon kwamishinan yada labarai na jihar Edo, Cif Charles Idahosa, ya fito ya yi magana game da sabanin da ake samu tsakanin gwamna Godwin Obaseki da Adams Oshiomhole.
Charles Idahosa ya na zargin cewa gwamnatin Godwin Obaseki ta na samun adawa ne daga shugaban jam’iyyar APC na kasa saboda ya ki bada damar taba baitul malin Edo.
Jaridar The Nation ta rahoto Charles Idahosa ya na cewa: “Matsalar ita ce ba za a iya amincewa da Oshiomhole ba, shiyasa ba za mu ba shi dama ko kadan a nan jihar Edo ba.”
“Gwamna ya yi aiki sosai. Su kansu masu fada da shi a lemar EPM ta mutanen Edo a karkashin jagorancin Adams Oshiomhole ba su zargin shi da gazawar aiki a ofis.” inji Idahosa.
Jagoran na APC mai mulki a jihar Edo ya ce babban laifin Obaseki shi ne kawai ya ki rabawa mutane kudi. “Zargin da ake jifarsa da shi kurum shi ne ya ki fitar da kudi a kashe.”
KU KARANTA: Yadda za ka rika samun labaran Legit.ng Hausa a shafinka da zarar an wallafa
Jaridar New Telegraph kuma ta rahoto cewa an samu baraka a gidan Fasto Osagie Ize-Iyamu a jam’iyyar APC, inda wasu daga cikin jiga-jigan jam’iyyar su ka fara juya masa baya.
Rahotanni sun bayyana cewa jagororin na APC a Jihar Edo sun daina goyon bayan takarar Ize-Iyamu ne bayan an samu labarin irin tirka-tirkar da ya ke fama da ita a gaban kotu.
Ana zargin cewa wadannan kusoshi na APC sun koma tafiyar Osaro Obazee ne. Obazee ya na cikin wadanda ake sa ran za su nemi tikitin jam’iyyar APC tare da Godwin Obaseki.
A wani kaulin kuma ana tunanin cewa ‘ya ‘yan jam’yyar APC sun fara dawowa daga rakiyar Osagie Ize-Iyamu ne bayan gwamna Obaseki ya gana da Bola Ahmed Tinubu kwanaki.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng