Tauraro Ronaldo ya saye gida mai dakin kallo da wurin wanka a kasar Sifen

Tauraro Ronaldo ya saye gida mai dakin kallo da wurin wanka a kasar Sifen

- Cristiano Ronaldo ya kashe fam miliyan £1.3 wajen sayen wani gida a Marbella

- Wannan katafaren gida ya na dauke da wani dakin kallo da kuma wurin wanka

- Duk Duniya babu ‘dan kwallon da ya ke da arziki irin Cristiano Ronaldo a yanzu

Rahotanni sun bayyana cewa shekarar da ta gabata Cristiano Ronaldo ya batar da miliyan £1.3 domin mallakar wani makeken gida a birnin Marbella da ke kasar Sifen.

Tsohon ‘dan wasan kwallon kafan na Real Madrid da Manchester United ya zarce sa’a a shekarar nan bayan ya zama ‘dan wasan farko a tarihi da ya mallaki Dala biliyan 1.

‘Dan wasan na kasar Portugal ya na da gidaje a Birane daban-daban na Duniya wadanda su ka hada da Ingila, Sifen, da Portugal, bayan kuma tarin motocin da ya mallaka.

KU KARANTA: Yadda za ka rika samun labaran Legit.ng Hausa a shafinka da zarar an wallafa

Wannan gida da Cristiano Ronaldo ya saya ya na da manyan dakuna hudu da wuraren shakatawa. A gefen gidan akwai wurin wasanni da kuma sansani domin hutawa.

Marbella wuri na da ya yi fice matuka wajen zuwa hutawa da jin dadi saboda gidajen rawa da ake da su. Girman wannan wuri bai wuce kilomita 27 ba, sannan babu jama’a sosai.

Jaridar UK Suk ta Birtaniyya ta ce Tauraron ya baza motoci na alfarma a wannan sabon gida. A yadda kasuwa ta ke yau, a kudin Najeriya wannan gida ya fi Naira miliyan 600.

Daga cikin motocin da Ronaldo mai shekaru 35 ya ke da su akwai Lamborghini Aventador LP 700-4, Rolls-Royce Phantom Drophead Coupe, da Audi Q7, da kuma Ferrari F430.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel