Rashin tsaro: Honarabul Victor Mela ya bukaci ‘Yan Majalisa su tashi tsaye

Rashin tsaro: Honarabul Victor Mela ya bukaci ‘Yan Majalisa su tashi tsaye

- Victor Mela Danzaria ya yi barazanar barin aikinsa a Majalisar Wakilan Tarayya

- ‘Dan Majlaisar na Billiri da Balanga ya ce dole ne a kawo karshen matsalar tsaro

- Mela ya bada wa’adin watanni biyu ga Majalisa ta tashi ta kare rayukan mutane

Honarabul Victor Mela mai wakiltar Balanga a Billiri a majalisar wakilan tarayya ya koka da halin rashin tsaron da ake ciki, inda ya ce akwai bukatar ‘yan majalisa su tashi tsaye.

Victor Mela ya bukaci ayi bincike game da kudin da ake kashewa bangaren tsaro. Mela ya zargi manyan jami’an tsaro da karkatar da dukiyar gwamnati wajen gina manyan gidaje.

“‘Duk inda ka je, muddin ka ga gida mai kyau, to ko dai na kyaftin ne ko kuma na Sufeta. Mutane da-dama su na samun kudi da wannan harka (rashin tsaro).” Inji ‘dan majalisar.

Hon. Mela ya ke cewa “Lokaci ya yi da za mu tashi tsaye a matsayinmu na ‘yan majalisar tarayya, mu yi aikin da ya rataya a kanmu, na ganin cewa sha’anin tsaron kasa ya inganta.

KU KARANTA: Takardun bogi: Alkali ya bada belin ‘Dan Majalisar Jihar Kwara a Kotu

Da ya ke jawabi a ranar Alhamis da ta wuce, Mela ya yi barazanar barin majalisa, ya ce:

“Ya shugaban majalisa da abokan aikina, ina so in fada cewa, zan ba kai na watanni biyu, idan wannan majalisa ba ta yi wa ‘Yan Najeriya wani abin kirki da ke nuna za a kawo karshen rashin tsaro ba, zan yi murabus.”

“Kuma da gaske na ke yin wannan magana. Ba za mu cigaba da zuwa nan, mu yi gum yayin da ake kashe jama’a ba. Abin ya yi yawa.” Ya tabbatar da cewa lallai da gaske ya ke yi.

A karshe Victor Mela ya ce: “Dole mu nunawa ‘Yan Najeriya cewa mu ‘yan majalisa ne.”

Dazu Legit.ng Hausa ta kawo rahoto cewa Muhammad Gudaji Kazaure ya yi Allah-wadai da yadda gwamnati ta karkata wajen yaki da ake yi da annobar COVID-19, ta manta da tsaro.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng