Alkali ya ba Audu Maikori gaskiya a shari’arsa da Gwamnatin Jihar Kaduna

Alkali ya ba Audu Maikori gaskiya a shari’arsa da Gwamnatin Jihar Kaduna

Wani kotun daukaka kara da ke zama a babban birnin tarayya Abuja, ya umarci gwamnatin jihar Kaduna ta biya diyya ga shugaban kamfanin Chocolate City Group, Audu Maikori.

Alkalan babban kotun da ke Abuja sun umarci gwamnatin Kaduna ta biya kudi har Naira miliyan 10.5 ga Audu Maikori a dalilin ci masa zarafi da tauye masa hakki da aka yi a 2017.

Alkali ya tabbatar da hukuncin da babban kotun tarayya ta yi kwanakin baya, inda aka zartar da cewa gwamnatin jihar Kaduna ta ketawa Maikori alfarma a lokacin da aka tsare shi.

Jami’an ‘yan sanda sun kama Audu Maikori ne a Legas a 2017, daga baya kuma aka yi gaba da shi zuwa Abuja, da sunan ya yada bayanan da za su iya tada hankalin mutanen Kaduna.

Kotun daukaka karar ta rage adadin diyyar da babban kotun tarayya ta yankewa gwamnati. A baya an umarci jihar Kaduna ta biya Maikori Naira miliyan 40, yanzu kudin ya dawo N10.5.

KU KARANTA: Yadda za ka rika samun labaran Legit.ng Hausa a shafinka da zarar an wallafa

Alkalai uku ne su ka zauna su ka yanke wannan hukunci a ranar Juma’a. Maikori ya tabbatar da wannan hukunci da kotu ta yi a dandalin tuwita kamar yadda Premium Times ta rahoto.

Ana zargin Maikori ya yi amfani da shafin tuwita wajen yada wasu labarai da ba gaskiya ba ne a game da rade-radin rikicin da ya barke tsakanin Makiya da mutanen Kudancin Kaduna.

A lokacin da aka cafke Maikori, ya shafe kwanaki akalla hudu a tsare kafin a gurfanar da shi a kotu. Daga baya ne ya yi nasarar samun beli bayan ya yi wa kotu kukan rashin lafiya.

Mista Maikori wanda Lauya ne kuma fitaccen ‘dan gwagwarmaya wanda ya ke yi wa mutanesa fafutuka, ya bayyana cewa burinsa kawai shi ne a samu zaman lafiya a jihar Kaduna.

A halin yanzu an shafe kwanaki fiye da 300 ana cigiyar wani Matashi, Abubakar Dadiyata a Kaduna. An sace Dadiyata wanda ya yi suna wajen sukar gwamantin APC ne tun 2019.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel