Shaidar digirin bogi: Mutum 3 sun maka gwamnan APC kotu
'Ya'yan jam'iyyar APC uku sun mika korafinsu gaban babban kotun tarayya da ke Abuja a kan zargin Gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki da satifiket din bogi.
Edobor Williams, Ugbesia Abudu Godwin da Amedu Dauda Anakhu sun shigar da kara a kan cewa kwalin digirin Gwamna Obaseki da ya yi ikirarin cewa ya same shi a jami'ar Ibadan, na bogi ne.
Ganin gabatowar zaben fidda gwani na jihar Edo da ke karatowa, an zargesa da bada shaidar digiri na bogi wanda ya ci karo da sashi na 18 sakin layi na 1 na kundun tsarin mulkin Najeriya.
"A don haka bai cancanci shugabanci ko fitowa takarar gwamnan jihar Edo ba" karkashin inuwar jam'iyyar APC.
KU KARANTA KUMA: Sabon tsarin Facebook: Yadda zaka rika ganin labaran Legit.ng Hausa a shafinka da dumi-dumi
Gwamna Obaseki ya bayyana wannan korafin da mara tushe balle makama.
Lauyan Obaseki, Alex Ejesieme (SAN) ya sanar da wakilin jaridar Daily Trust cewa kungiyarsa ta shirya kalubalantar wannan dokar a kotu.
Wannan na zuwa ne bayan jam'iyyar APC reshen jihar Edo ta maka Adams Oshiomhole da kwamitin ayyukan na jam'iyyar a gaban kotu.
KU KARANTA KUMA: Yanzu-yanzu: Saudiyya za ta mayar da dokar kulle, ta bada sharudda 4
An zargesu da mika tikitin neman kujerar gwamnan jihar a karkashin APC a hannun Fasto Osagie Ize-Iyamu.
A jihar Edo, jam'iyyar APC ta kasu gida biyu tun a shekarar da ta gabata bayan rikicin da ya barke tsakanin Obaseki da Oshiomhole.
A baya Legit.ng ta rahoto cewa mataimakin gwamnan jihar Edo, Kwamared Philip Shaibu, ya bada tabbacin cewa Gwamna Godwin Obaseki zai yi nasarar a kowanne irin zaben fidda gwani a jihar koda kuwa bai shirya ba.
A wata takarda da mataimakin gwamnan ya fitar a Abuja, mai bada shawararsa na musamman a kan yada labarai, Benjamin Atu, ya ce rawar da gwamnatinsa ta taka kadai ya isa yasa su samu nasara a zabe mai zuwa koda kuwa ba a bada dogon lokaci ba na shiri.
Ya ce gwamnatin Obaseki za ta so a yi kato bayan kato wajen zaben fidda gwani. Hakan zai taka rawar gani wurin dakile yaduwar annobar korona.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng