Ku halaka min dukkan 'yan bindiga - Shugaban NAF ya umarci soji

Ku halaka min dukkan 'yan bindiga - Shugaban NAF ya umarci soji

Shugaban rundunar sojin saman Najeriya, Air Marshall Sadique Abubakar ya bada umarni ga dakarunsa da su binciko tare da halaka 'yan bindigar da suka addabi Katsina.

Ya sanar da hakan ne a ranar Alhamis inda ya umarcesu da mika rahoton ayyukansu na kowanne mako.

A yayin ziyara da ya kai wa rundunar Operation Hadarin Daji a Katsina, Abubakar ya ce, "Dole ne mu nemo inda 'yan bindigar suka boye tare da halaka su.

"Kada mu saurara har sai jama'a sun koma yadda suke a da ba tare da tsoron hari daga 'yan bindiga ko masu garkuwa da mutane ba," yace.

Ku halaka min dukkan 'yan bindiga - Shugaban NAF ya umarci soji
Ku halaka min dukkan 'yan bindiga - Shugaban NAF ya umarci soji Hoto: PM News
Asali: UGC

Ya ce za a samar da dukkan kayayyakin da dakarun ke bukata don ba za a bar 'yan bindigar su numfasa ba.

KU KARANTA KUMA: Sabon tsarin Facebook: Yadda zaka rika ganin labaran Legit.ng Hausa a shafinka da dumi-dumi

Yayin da yake rokar mazauna yankunan da su taimaka da bayanan sirri game da 'yan bindigar, Abubakar ya ce, "Yan bindigar ba aljanu bane hakazalika masu garkuwa da mutane.

Idan aka bamu bayanan sirri, hakan zai taimaka mana da kasar baki daya."

Gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari ya ce ba zai sake neman sasanci da 'yan bindiga ba a fadin jihar.

Gwamnatin ta janye sasancin da take nema da 'yan bindigar sakamakon jerin hare-haren da ake kai wa kauyukan jihar.

Masari ya ce tunda 'yan bindigar ba su karrama yarjejeniyar da suka yi ba da farko, gwamnatin ba za ta kara neman zaman lafiya da su bai.

Masari ya ce gwamnatin jihar ta sa hannu a kan yarjejeniya da 'yan bindigar inda suka yi alkawarin tuba tare da barin yankin arewa maso yamma.

Amma kamar yadda yace, "Sun kasa karrama yarjejeniyar da muka yi kuma sun ci amanar jama'ar jihar Katsina."

KU KARANTA KUMA: COVID-19: Akwai yuwuwar jihohi 32 su kasa biyan ma'aikata bayan annobar

Gwamnan ya ce wasu daga cikin 'yan bindigar 'yan asalin Kaduna, Zamfara har da jamhuriyar Nijar ne.

Ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta samar da isasshen tsaro da kayan aiki don karar da 'yan bindigar a jihar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel