Operation Accord: Sabon atisayen rundunar soji ya halaka 'yan bindiga 392

Operation Accord: Sabon atisayen rundunar soji ya halaka 'yan bindiga 392

- Rundunar sojin Najeriya karkashin Operation Accord sun halaka 'yan bindiga da dama a yankunan arewa maso yamma da arewa ta tsakiya na kasar

- An tanadi shirin ne don halaka 'yan bindigar da ke tserewa sakamakon luguden ruwan wutar da dakarun soji ke musu

- Hakazalika a yankin arewa maso yamma, dakarun soji da sauran jami'an tsaro sun matsanta wa 'yan ta'adda ta sama da tudu ta karkashin atisayen Operation Lafiya Dole

A kalla 'yan bindiga 392 ne rundunar sojin Najeriya karkashin sabon atisayen Operation Accord suka halaka a yankunan arewa maso yamma da arewa ta tsakiya na kasar.

Shugaban sashin yada labarai na rundunar sojin, Manjo Janar John Enenche, ya sanar da manema labarai a garin Abuja cewa daga hedkwatr tsaro ta kasa aka kirkiro Operation Accord.

KU KARANTA KUMA: Sabon tsarin Facebook: Yadda zaka rika ganin labaran Legit.ng Hausa a shafinka da dumi-dumi

An kirkiro shirin ne don halaka 'yan bindigar da ke tserewa sakamakon luguden ruwan wutar da dakarun soji ke musu.

Operation Accord: Sabon atisayen rundunar soji ya halaka 'yan bindiga 392
Operation Accord: Sabon atisayen rundunar soji ya halaka 'yan bindiga 392 Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

Kamar yadda yace, "Sakamakon kokarin dakarun sojin Najeriya a yankin arewa maso yamma, rundunar sojin sama da na kasa sun halaka 'yan bindiga 392.

"Hakan ya zama babbar tawaya ga 'yan bindiga a yankin. Wadanda suka yi yunkurin tserewa kuwa sun samu ruwan wuta daga sojin kasa.

"Daga nan ne aka kaddamar da atisayen Operation Accord a ranar 1 ga watan Yunin 2020".

Ya kara da cewa, "A yankin arewa maso yamma, rundunar sojin Najeriya da sauran jami'an tsaro sun matsanta wa 'yan ta'adda ta sama da tudu ta karkashin atisayen Operation Lafiya Dole.

"Wannan ya kawo karewar manyan kwamandojin Boko Haram da kuma tarwatsewar makaman 'yan ta 'addan."

KU KARANTA KUMA: Rayuka 3 na taba kashe ba 16 ba - Shahararren dan kungiyar asiri ya yi bayani

Hakazalika, sansanin mayakan ya kasance cike da tashin hankali sakamakon rashin shugabanninsu.

Enenche ya kara da cewa, "Operation Accord runduna ce ta hadin guiwa ta jami'ai tsaro a yankin arewa maso yamma da arewa ta tsakiya don shawo kan matsalar 'yan bindiga da sauran laifuka."

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel