Edo 2020: Obaseki zai yi nasara a kowanne irin zaben fidda gwani da za a yi - Shaibu

Edo 2020: Obaseki zai yi nasara a kowanne irin zaben fidda gwani da za a yi - Shaibu

Mataimakin gwamnan jihar Edo, Kwamared Philip Shaibu, ya bada tabbacin cewa Gwamna Godwin Obaseki zai yi nasarar a kowanne irin zaben fidda gwani a jihar koda kuwa bai shirya ba.

A wata takarda da mataimakin gwamnan ya fitar a Abuja, mai bada shawararsa na musamman a kan yada labarai, Benjamin Atu, ya ce rawar da gwamnatinsa ta taka kadai ya isa yasa su samu nasara a zabe mai zuwa koda kuwa ba a bada dogon lokaci ba na shiri.

Ya ce gwamnatin Obaseki za ta so a yi kato bayan kato wajen zaben fidda gwani. Hakan zai taka rawar gani wurin dakile yaduwar annobar korona.

"Duk da wannan tabbacin na nasarar Gwamna Obaseki, bamu shirya yin zaben kato bayan kato ba a zaben fidda gwani.

"Dalilin da yasa muke son yin wanda ba kato bayan kato ba, bamu son samun nasara amma kuma da kalubalen rashin cikakkiyar lafiyar jama'a," yace.

Edo 2020: Obaseki zai yi nasara a kowanne irin zaben fidda gwani da za a yi - Shaibu
Edo 2020: Obaseki zai yi nasara a kowanne irin zaben fidda gwani da za a yi - Shaibu Hoto: TVC
Asali: Twitter

Ya kara da cewa, wasu daga cikin kafafen yada labarai su ke assasa wasu al'amura tare da tada wutar tashin hankali a fadin jihar.

KU KARANTA KUMA: Sabon tsarin Facebook: Yadda zaka rika ganin labaran Legit.ng Hausa a shafinka da dumi-dumi

Kamar yadda yace, Gwamnan ya dage wajen dakile yaduwar annobar korona a fadin jihar Edo.

"A matsayin babban jami'in tsaron jihar Edo, gwamnan ya yanke hukuncin kiyaye rayukan 'yan jihar."

A baya Legit.ng ta kawo maku cewa Gwamna Godwin Obaseki na jihar Edo ya ce a lokacin da wanda ya gada, Adams Oshiomhole ya yi takarar gwamnan jihar a 2017, bashi da kudi.

Oshiomhole, tsohon shugaban kungiyar kwadago ta kasa wanda ya nemi kujerar gwamnan jihar Edo karkashin jam'iyyar AC ya sha mugun kaye a hannun Oserheimen Osunbor na jam'iyyar PDP.

Amma bayan kalubalantar nasarar Osunbor, kotu ta kwace karagar mulkin jihar tare da mika ta hannun Oshiomhole bayan shekara daya.

A yayin zantawa da manema labarai bayan mika fom din nuna ra'ayin takarar gwamnan jihar Edo a karkashin by APC, Obaseki ya ce babban kuskure ne idan aka ce ya ci amanar Oshiomhole.

KU KARANTA KUMA: Yanzu-yanzu: Majalisar wakilai ta yi wa shugabannin tsaro kiran gaggawa

Gwamnan ya ce ba wai taimakon Oshiomhole ya yi kadai wurin zama gwamna ba kadai, ya sadaukar da abubuwa masu tarin yawa don tabbatar da cewa ya zama shugaban jam'iyyar APC mai mulki.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel