Yadda aka shiryawa babban alkali gadar zare ya saki rikakkun ma su garkuwa da mutane
- Alkalin alkalai na jihar Katsina, Musa Abubakar, ya sallami wasu rikakkun ma su garkuwa da mutane ta hanyar bayar da su belinsu
- Babban alkalin ya rattaba hannu kan takardun neman belin ma su laifin tun kafin zaman sauraron bukatar neman belinsu da lauya ya rubuta
- Kungiyar lauyoyi reshen jihar Katsina ta ce ta yi matukar mamakin yadda babban alkali zai ce an yaudare shi ya bayar da belin da manyan ma su laifi
Wani ma'aikaci a ma'aikatar shari'a ta jihar Katsina ya ce an yaudari babban alkalin alkalan jihar Katsina, Musa Abubakar, wajen saka hannu a kan takardun belin wasu rikakkun ma su garkuwa da mutane guda biyu da aka kama.
Kabir Shuaibu, babban rijistaran babbar kotun jiha, ya ce babbar kotun jiha ta '9' ba ta kai ga zama domin sauraron bukatar neman bayar da belin ma su laifin ba kafin babban alkalin ya bada belinsu.
Ya ce an hada baki da wasu ma'aikatan kotun wajen satar takardun neman beli da aka gabatarwa babban alkalin har ya rattaba hannu a kansu.
Batun sakin gagararrun ma su garkuwa da mutanen ya haddasa barkewar cece - kuce saboda sune aka kama da zargin sace mahaddacin Qur'ani, Ahmed Sulaiman.
An sace Malam Suleiman a watan Maris na shekarar 2019 a kan hanyar Sheme zuwa Kankara a jihar Katsina.
Jami'an tsaro sun kama wadanda su ka sace shi tare da gurfanar da su a gaban babbar kotun jihar Katsina.
Lauya Yusuf Daura, daya daga cikin wadanda aka kama bisa zarginsu da hannu a kitsa belin ma su garkuwa da mutane ya kare kansa.
DUBA WANNAN: Sabon tsarin Facebook: Yadda zaka rika ganin labaran Legit.ng Hausa a shafinka da dumi-dumi
Yusuf Daura, mamba a kungiyar lauyoyi ta kasa (NBA) reshen jihar Katsina, ya ce shi kansa a matsayinsa na lauyan wadanda ake zargi bai san yadda aka yi har aka saki ma su laifin ba tun kafin zaman kotu domin sauraron bukatarsa na neman belinsu.
Lauyan ya bayyana cewa shi kansa ya yi mamakin jin cewa alkali ya saka hannu a takardun bayar da su beli tun kafin lokacin kotu na sauraron kararsu.
Da ya ke ganawa da manema labarai a Katsina, sakataren kungiyar NBA reshen jihar Katsina, Ibrahim Babangida, ya ce babban abinda ya fi daure mu su kai shine yadda alkalin alkalai zai saka hannu a kan takardun beli ba tare da karanta sharudan bayar da belin ba.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng