Gwamna Nasir El-Rufai ya na ganawa da Sarakuna game da maganar bude Gari

Gwamna Nasir El-Rufai ya na ganawa da Sarakuna game da maganar bude Gari

- Gwamnan Jihar Kaduna ya shiga taro da Sarakunan kasa a yau da safe

- Gwamna Nasir El-Rufai zai duba yadda za a bi wajen bude Jihar Kaduna

- Tun a watan Maris aka rufe Kaduna saboda takaita yaduwar COVID-19

A safiyar yau Alhamis mu ka ji labari cewa gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufai, ya shiga taro na musamman da Sarakunan gargajiya da ke jihar Kaduna.

Mai girma gwamna Nasir El-Rufai ya na wannan taro da Sarakunan kasarsa ne domin duba yadda zai bude Kaduna bayan an shafe tsawon lokaci jihar ta na rufe.

Gwamnatin jihar Kaduna ta bada sanarwar wannan zama da aka shiga da safiyar yau, 4 ga watan Mayu, 2020. Gwamnatin ta fitar da jawabi ne ta dandalin tuwita dazu.

Kamar yadda mu ka samu labari daga shafin gidan gwamnatin Kaduna a tuwita, an shiga wannan taro ne da kimanin karfe 11:00 a wani dakin taron da ke fadar.

KU KARANTA: Yadda za ka rika samun labaran Legit.ng Hausa a shafinka da zarar an wallafa

Legit.ng Hausa ta fahimci cewa fiye da Sarakuna goma ne su ke halartar wannan zama da ake yi a matsayinsu na masu ruwa da tsaki a lamarin al’ummar jihar.

Haka zalika mataimakiyar gwamna, Dr. Hadiza Sabuwa Balarabe ta samu zama a wannan taro. Kowanensu ya na dauke da takunkumin rufe fuska na kare lafiya.

Wadanda su ka halarci wannan taro sun zauna ne nesa-nesa da juna. Sai dai kawo yanzu babu labarin matsayar da aka cin ma a wajen wannan taro da aka shiga.

Gwamnatin jihar Kaduna ta yi alkawarin tattaunawa da masu ruwa da tsaki domin ganin yaushe ne ya fi dacewa a bude gari da kuma yadda za a cin ma matakin.

A jawabin da gwamna El-Rufai ya yi a cikin makon nan, ya tabbatar da cewa har yanzu ba a kai ga bude kasuwanni da dakunan ibada a jihar Kaduna ba tukuna.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel