COVID-19: Gwamna Masari ya dakatar da daukar aiki, gudanar da manyan ayyuka da karin girma a Katsina

COVID-19: Gwamna Masari ya dakatar da daukar aiki, gudanar da manyan ayyuka da karin girma a Katsina

Gwamnan jihar Katsina, Rt Hon Aminu Bello Masari ya bada umarnin dakatar da daukar sabbin ma'aikata da karin girma kowanne iri ga ma'aikata a matakin jihar ko kananan hukumomi.

Gwamnan ya kara da dakatar da dukkan manyan ayyuka banda wadanda ake matukar bukata.

Wannan na kunshe a wata takarda mai kwanan wata 22 ga watan Mayu daga ofishin Shugaban ma'aikatan jihar.

Wannan hukuncin, kamar yadda takardar ta bayyana, ya biyo bayan kalubalen da annobar korona ta yi kawowa jihar.

COVID-19: Gwamna Masari ya dakatar da daukar aiki, manyan ayyuka da karin girma a Katsina
COVID-19: Gwamna Masari ya dakatar da daukar aiki, manyan ayyuka da karin girma a Katsina Hoto: Aminu Bello Masari
Asali: Twitter

KU KARANTA KUMA: Sabon tsarin Facebook: Yadda zaka rika ganin labaran Legit.ng Hausa a shafinka da dumi-dumi

Kamar yadda wasikar ta bayyana, "Sakamakon faduwar farashin man fetur a fadin duniya saboda annobar korona, mai girma gwamnan jihar Katsina, Rt Hon Aminu Bello Masari ya bukaci kara duba kasafin kudin jihar na 2020 tare da kai wadannan matsayar:

1. An dakatar da daukar aiki a matakin jihar da kananan hukumomi na jihar Katsina.

2. Dakatar da karin girma ga ma'aikatan jihar da na kananan hukumomi.

3. Dakatar da dukkan manyan ayyuka banda wadanda ake matukar bukata.

"A don haka ake bukatar mika abinda takardar nan ta kunsa ga jama'a da ta shafa don sun sani."

KU KARANTA KUMA: Covid-19: NNPC ta kaddamar da manhajar zakulo masu cutar

A wani labarin na daban, mun ji cewa gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari, ya ce ba zasu sake wani sulhu da yarjejeniya da yan bindiga ba a jihar tunda suka saba wanda akayi da su a baya.

Ya ce gwamnatin jihar ta yi yarjejeniya da yan bindigan kuma sun yi alkawarin tuba tare da fita daga jihar amma basu cika alkawarin ba. Mayaudara ne, a cewarsa.

Yayinda yake hira da BBC Hausa a Instagram, gwamnan ya ce daga wasu cikin yan bindigan, suna zuwa ne daga jihar Kadina, Zamfara, har ma daga kasar Nijar.

Masari ya ce shine gwamna na farko da ya fara sulhu da yan bindiga a shekarar 2016 kuma sun fara cika alkawari kafin kuma suka yaudari gwamnati.

Ya yi kira ga gwamnatin tarayya ta samar da isasshen jami'an tsaro da kayan aiki saboda a samu nasarar yaki da barandanci a jihar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel