An sanar da rasuwar tsohon Gwamnan Jihar Ondo Bamidele Olumilua
- Tsohon gwamna Bamidele Olumilua ya cika ya na da shekara 80
- Tsohon gwamnan Ondon ya mutu ne a gidansa da ke jihar Ekiti
- Bamidele Olumilua ya yi mulki tsakanin shekarar 1992 da 1993
Cif Bamidele Olumilua, wanda ya yi mulki a tsohuwar jihar Ondo ya rasu. Marigayin ya bar Duniya ya na da shekaru kimanin 80 da haihuwa.
Bamidele Olumilua shi ne gwamna na goma a jeringiyar wadanda su ka yi mulki a Ondo. Olumilua ya mulki jihar ne tsakanin 1992 da 1993.
Kamar yadda mu ka samu labari, jaridar The Tribune ce ta fara fitar da rahoton mutuwar wannan dattijon ‘dan siyasan a yau 4 ga watan Yuni, 2020.
Babban ‘Dan marigayin, Muyiwa Olumilua ya bada sanarwar mutuwar tsohon. Olumilua kwamishina ne na watsa labarai a gwamnatin Ekiti.
KU KARANTA: Hukumar 'Yan Sanda ta PSC ta rasa wani daga cikin Jami'an ta
Kwamishinan yada labarai da ziyarar buda ido na gwamnatin Fayemi ya bayyana cewa mahaifin na su ya mutu ne a farkon yau Alhamis a gida a Ekiti.
Cif Olumilua ya na cikin wadanda su ka lashe zaben da gwamnatin sojan Janar Ibrahim Badamasi Babangida ta shirya a farkon shekarar 1992.
Olumilua ya dare mulki ne a karkashin jam’iyyar SDP inda ya doke ‘dan takarar NRC. A shekarar 1993 ne Janar Sani Abacha ya sauke duka gwamnoni.
Olumilua ya karbi mulki ne a hannun Sunday Abiodun Olukoya. Bayan gajeren wa’adin da ya yi, ya dawo siyasa a 1999 inda ya shiga jam’iyyar PDP.
Marigayin ya rike mukami a gwamnatin jam’iyyar PDP, amma daga baya ya sauya-sheka. Kafin rasuwarsa, jam’iyyar siyasar karshe da ya yi ita ce AC.
KU KARANTA: Yadda za ka rika samun labaran Legit.ng Hausa a shafinka
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng