An gurfanar da Hon. Ahmed Ndakene a gaban kotu, ya samu belin N5m

An gurfanar da Hon. Ahmed Ndakene a gaban kotu, ya samu belin N5m

A ranar Laraba, 3 ga watan Yuni, 2020, aka gurfanar da ‘dan majalisar wakilan tarayya, Ahmed Abubakar Ndakene a gaban Alkali, ana zarginsa da amfani da takardun shaidar karya.

Jaridar Daily Trust ta ce Alkalin kotu ya bada belin Honarabul Ahmed Abubakar Ndakene a mai wakiltar mazabar Edo/Moro/Pategi a kan kudi Naira miliyan 5 bayan an saurari karar.

Abokin takarar ‘dan majalisar a karkashin PDP a zaben 2019, Mahmud Hassan Babako ne ya shigar da karar Abubakar Ndakene bisa zargin cewa ya yi karya game da takardunsa.

Babako ya shaidawa kotu cewa ‘dan majalisar ya yi wa hukumar zabe na kasa watau INEC karya a takardun da ya gabatar mata kafin ya shiga takarar kujerar majalisar da ya yi nasara.

Mahmud Hassan Babako ya na zargin ‘dan majalisar wakilan da yi wa hukuma karya wajen darewa kujerar da ya ke kai, wanda hakan ya sabawa dokar kasa da kuma tsarin mulki.

Da aka dawo zama a jiya, lauyan wanda ya ke kara, Labio Orji ya roki Alkali ya kira Ndakene, Mai kare wanda ake tuhuma, Alex Edim, ya roki kotu ta maida lamarin gaban ‘yan sanda.

KU KARANTA: COVID-19: Ma’aikata sun bar ofis bayan mutuwar Jami’in NDDC

An gurfanar da Hon. Ahmed Ndakene a gaban kotu, ya samu belin N5m
Shugaban Majalisar Wakilai Hoto: House of Reps
Asali: Twitter

Edim ya ce: “Duk korafin da aka gabatar yau, za a iya kai su gaban ‘yan sanda ayi bincike kafin a dauki wani mataki. Sashe na 106 da 89 ba su ba wani mutum damar shigar da kara ba.”

Lauyan wanda ake tuhuma ya hakikance a kan cewa ‘yan sanda ne za su binciki wannan zargi da ke kan wuyan ‘dan majalisar ko kuma a nemi izni daga ofishin ministan shari’a na kasa.

A karshe lauyan ‘dan majalisar ya roki kotu ta yi waje da karar, ta maida maganar wajen jami’an ‘yan sanda. Alkali mai shari’a Inuwa Maiwada, bai gamsu da wannan roko na lauyan ba.

Maiwada ya ce babu inda sashen dokar da aka ambata ta ce ‘yan sanda ne kadai za su iya yin bincike a kan zargin. Alkalin ya ce ya kamata kotu ta cigaba da tsare wanda ake tuhuma.

Ganin yadda ake fama da annobar COVID-19, kotu ta bada belin ‘dan majalisar kan Naira miliyan biyar. Sannan an bukaci wani mutum ya tsaya masa. Za a sake zama a mako mai zuwa.

KU KARANTA: Yadda za ka rika samun labaran Legit.ng Hausa a shafinka

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel