Kaduna: 'Yan bindiga sun kashe mutane 9, sun raunata wasu da dama a sabon harin da su ka kai

Kaduna: 'Yan bindiga sun kashe mutane 9, sun raunata wasu da dama a sabon harin da su ka kai

'Yan bindiga sun sake kai hari a kauyen Tudu da Agwala Dutse da ke karkashin karamar hukumar Kajuru inda su ka kashe a kalla mutane tara tare da raunata wasu da dama.

Wannan sabon hari na zuwa ne a kasa da sati uku da kai wasu munanan hare - hare a kauyukan karamar hukumar Kajuru.

Jaridar 'The Nation' ta rawaito cewa 'yan bindigar sun kai hari kauyen Tudu da sanyin safiyar ranar Laraba, inda su ke bude wuta ga duk wanda su ka gani.

Kungiyar SOKAPU ta 'yan asalin mutanen kudancin jihar Kaduna sun yi zargin cewa a kalla gawar mutane 30 aka samu ta fara rubewa a cikin daji bayan wasu hare - hare da makiyaya su ka kai a wasu kauyuka 15 da ke yankin.

Wata majiya a Kajuru ta shaidawa jaridar 'The Nation' cewa 'yan bindga sun kai hari kauyen Tudu da misalin karfe 5:00 na safiyar ranar Laraba.

Majiyar ta ce 'yan bindiga sun hau harbin duk wanda su ka gani a yayin da mazauna kauyen ke gudun neman mafaka domin tsira da ransu.

"Tabbas an kai hari kauyen Tudu da Agwala Dutse da misalin karfe 5:00 na safiyar yau (Laraba). An kashe mutane da dama tare da raunata wasu ma su yawa," a cewar majiyar.

Kaduna: 'Yan bindiga sun kashe mutane 9, sun raunata wasu da dama a sabon harin da su ka kai
Nasir El-Rufa'i
Asali: Twitter

Shugaban karamar hukumar Kajuru, Mista Cafra Caino, ya tabbatar da kisan mutane tara yayain harin da aka kai.

Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa'i, ya dade da bayyana cewa ba zai yi sulhu da 'yan bindigar da su ke kai hare - hare a sassan jihar Kaduna ba.

DUBA WANNAN: Mai laifi ya jagoranci 'yan sanda zuwa wurin da su ka binne gawar lauyan da su ka kashe

A ranar Talata ne Legit.ng ta wallafa labarin cewa gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari, ya ce ba zai kara yin sulhu da 'yan bindiga ba saboda cin amanar da aka yi wa gwamnatinsa.

A cewar gwamnan, barayin da ke fashi a dazuka sun ci amanar yarjejeniyar zaman lafiya da aka kulla da su.

Yayin hirarsa da sashen Hausa na BBC, Masari ya ce daga cikin 'yan bindigar da ke kai hare - hare a jihar Katsina akwai wadanda su ka fito daga jihar Kaduna da Zamfara da 'yan Nijar.

Masari ya bayyana cewa gwamnatinsa ce ta fara zuwa da tsarin yin sulhu da 'yan bindiga a shekarar 2016.

Gwamna Masari ya ce da farko sulhun ya yi tasiri wajen dawo da zaman lafiya a jihar Katsina kafin daga bisani 'yan bindigar su ci amanar gwamnati.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel