Jerin sunaye: Filayen jiragen sama 5 da za su fara aiki

Jerin sunaye: Filayen jiragen sama 5 da za su fara aiki

- Gwamnatin tarayya ta amince da bude filayen jiragen sama biyar a fadin kasar nan don dawo da zirga-zirgar jirage a kasar

- Captain Musa Nuhu, shugaban NCAA ya bada wannan sanarwar a wata wasika mai kwanan wata 1 ga watan Yunin 2020

- NCAA din ta tabbatar da cewa dukkan filayen jiragen saman dole su kiyaye dokokin dakile yaduwar Covid-19

Gwamnatin Najeriya ta amince da bude filayen jiragen sama biyar don dawo da zirga-zirgar jirage a cikin kasar nan daga ranar 21 ga watan Yuni.

Kaftin Musa Nuhu, shugaban hukumar sufurin jiragen sama (NCAA) ya sanar da hakan a wata wasika mai kwanan watan 1 ga Yunin 2020, Daily Trust ta ruwaito.

Gwamnatin ta bayyana cewa, an rufe filayen jiragen saman ne don dakile yaduwar muguwar cutar coronavirus kuma za a ci gaba da hana tashi ko saukar jiragen ketare.

Jerin sunaye: Filayen jiragen sama 5 da za su fara aiki
Jerin sunaye: Filayen jiragen sama 5 da za su fara aiki Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

Kamar yadda NCAA ta bayyana, filayen jiragen saman da za a bude sune:

1. Filin sauka da tashin jiragen sama na Murtala Muhammed da ke Legas.

2. Filin jirgin Nnamdi Azikiwe da ke Abuja.

3. Filin tashi da saukar jiragen saman da ke Fatakwal, Omagwa a jihar Ribas.

4. Filin dauka da tashin jiragen sama na Mallam Aminu Kano.

5. Filin sauka da tashin jiragen sama na Sam Mbakwe da ke Owerri.

KU KARANTA KUMA: Motoci uku muka siyar kafin karbo mahaifinmu - Dan shugaban CAN ya bayyana

NCAA ta ce dukkan filayen jiragen saman dole su yi biyayya ga dokokin masana lafiya na dakile yaduwar muguwar cutar coronavirus.

Hukumar ta bayyana cewa har yanzu ba za a amince da sauka ko tashin jiragen sama ba na kasashen ketare.

Tun a ranar 27 na watan Maris aka rufe filayen jiragen saman kasar nan don dakile yaduwar muguwar cutar coronavirus.

A wani labarin kuma, sabuwar dokar kulle ta Ingila ga 'yan kasa ta haramta jima'i da dan waje wanda ba dan gida ba a yayin da gari yake kulle.

A ranar Litinin, 1 ga watan Yunin 2020, gwamnatin Ingila ta bayyana sabuwar dokarta da ta haramta shakatawa da jama'a da ba na gida ba a yayin da dokar kulle ke aiki.

Sabuwar dokar ta ce: "Babu wanda aka amince ya yi wani taro a waje ko a gida wanda ya kai mutum biyu ko fiye."

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel