Wata sabuwa: Ana rikita-rikita a kan shugabancin kotun daukaka kara

Wata sabuwa: Ana rikita-rikita a kan shugabancin kotun daukaka kara

Akwai shirye-shiryen dakatar da Monica Bolna'an Dongban-Mensem daga zama shugabar kotun daukaka kara, jaridar The Cable ta ruwaito.

An tattaro cewa akwai yunkurin da ake yi kuma na nada Mohammed Lawal Garba, wanda ya jagoranci kararrakin zaben shugaban kasa na 2019 a maimakonta.

Duk da cewa ana ta cece-kuce a kan Dongban-Mensem a matsayinta na kiristar arewa yayin da Garba yake Musulmi. The Cable ta gano cewa al'amarin ya ginu ne a kan siyasa, kabilanci da addini.

Hukumar shari'a ta tarayya ta bayyana Dongban-Mensem da Lawal a matsayin wadanda za su iya maye gurbin Zainab Bulkachuwa wacce ta yi murabus a Maris din 2020 bayan ta cika shekaru 70.

Wata sabuwa: Ana rikita-rikita a kan shugabancin kotun daukaka kara
Wata sabuwa: Ana rikita-rikita a kan shugabancin kotun daukaka kara Hoto: The Cable
Asali: UGC

A halin yanzu Dongban-Mensem ce babbar alkali a kotun tarayya kuma 'yar asalin jihar Filato ce.

Amma kuma, har yanzu shugaban kasa Muhammadu Buhari bai tura sunanta majalisa don tabbatarwa a kusan watanni uku da suka gabata.

A maimakon hakan, ya nada ta a wani matsayi na wucin-gadi na wasu watanni uku wanda zai iya kaiwa har watan Satumban 2020.

Majiyarmu ta gano cewa, mutanen Buhari ne basu son nadin Dongban-Mensem.

An gano cewa mashawartan Buhari na bin diddigi don kawo hanyar hana Dongban-Mensem hawa wannan matsayi tare da bai wa Garba dama.

An bincikin shaidar hidimar kasarta amma an gano cewa tabbas ta yi hidimar a shekarar 1980 zuwa 1981.

Garba, wanda aka fi so ya shugabanci shari'ar zabe ta shugaban kasa a watan Satumban 2019.

KU KARANTA KUMA: Zargin damfara: Rundunar 'yan sanda ta yi wa shugaban APC kiran gaggawa

A wani laari na daban, mun ji cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya ce Najeriya za ta tsaya tsayin daka wajen goyon bayan Dakta Akinwumi Adesina a kokarin sa na sake zama shugaban bankin ci gaban Afirka, AfDB.

Hakan ya fito ne daga bakin mai ba shugaban kasa shawara ta musamman kan harkokin yada labarai, Mista Femi Adesina.

Cikin sanarwar da Mista Femi ya gabatar, ya ce Buhari ya bayar da tabbacin ne a fadarsa ta Abuja, a ranar Talata yayin da ya karbi bakuncin Dr Adesina wanda ya kai masa ziyarar ban girma.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel