Zargin damfara: Rundunar 'yan sanda ta yi wa shugaban APC kiran gaggawa

Zargin damfara: Rundunar 'yan sanda ta yi wa shugaban APC kiran gaggawa

Rundunar 'yan sandan jihar Neja a ranar Talata ta yi kiran gaggawa ga Mohammed Jibril Imam, shugaban jam'iyyar APC na jihar a kan zarginsa da ake da almundahanar kudi.

Kamar yadda kwamishinan 'yan sandan jihar ya bayyana, ana zargin jigon APC din da wawurar kudin jam'iyyar tun da ya hau mulkinta a 2015.

Usman ya sanar da kamfanin Dillancin Labaran Najeriya a Minna cewa an mika korafi a kan jigon jam'iyyar APC din sakamakon zarginsa da ake yi da lamushe kudaden jam'iyyar tun daga kan na fom da 'yan takara ke siya.

Ya ce masu korafin sun zargi shugaban jam'iyyar da kashe kudi babu dalili.

Zargin damfara: Rundunar 'yan sanda ta yi wa shugaban APC kiran gaggawa
Zargin damfara: Rundunar 'yan sanda ta yi wa shugaban APC kiran gaggawa Hoto: Premium Times
Asali: UGC

Kamar yadda yace, wasu mambobin majalisar zartarwar jam'iyyar na jihar ne suka mika korafin inda suke zargin shugaban da amfani da kujerarsa ba ta yadda ya dace ba.

"Muna bincikar lamarin kuma za mu gano tushensa. Za mu gano cewa idan akwai gaskiya a cikin ikirarin masu korafin.

"Yan sandan Najeriya na da alhakin binciken duk wani nau'i na rashin gaskiya da duk wani dan kasa ya kawo korafi. Shiyasa muke yin hakan," yace.

"Za mu duba al'amarin cike da kwarewa don tabbatar da an yi adalci ga kowa," ya kara da cewa.

Duk kokarin Kamfanin Dillancin Labaran Najeriyan na son jin ta bakin shugaban jam'iyyar, lamarin bai yuwu ba.

KU KARANTA KUMA: El-Rufai ya shawarci matarsa a kan yadda za ta yi da tsagerun Twitter

A wani labari na daban mun ji cewa, a ranar Talata, 2 ga watan Yuni, 2020, majalisar dattawan Najeriya ta tabbatar da Dr. Muheeba Farida Dankaka a matsayin shugabar hukumar raba dai-dai ta kasa watau FCC.

Majalisa ta amince da mukamin da shugaban kasa ya ba Farida Dankaka da wasu mutane 36 a hukumar da ke da alhakin ganin an yi adalci wajen raba arzikin kasa da mukami.

‘Yan majalisar kasar sun yi na’am da wannan mataki ne bayan sun yi la’akari da wani rahoto da shugaban kwamitin da ke lura da aikin hukumar, Danjuma La’ah ya gabatar dazu.

Bisa dukkan alamu kwamitin sanata Danjuma La’ah mai wakiltar Kaduna ta tsakiya a karkashin jam’iyyar PDP ya yi na’am da wadannan nadin mukamai da shugaban kasar ya yi.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel