Bincike: Adadin kudin da Majalisa, tsofaffin Shugabanni da Jihohin Neja-Delta su ka ci

Bincike: Adadin kudin da Majalisa, tsofaffin Shugabanni da Jihohin Neja-Delta su ka ci

- Najeriya ta kashe tiriliyan 11 kan jihohin Neja-Delta da biyan 'Yan Majalisa da Sanatoci

- Rahotanni sun ce an kashe wadannan tarin kudin ne tsakanin 1999 zuwa shekarar bara

Daga shekarar 1999 da aka dawo mulkin farar hula a Najeriya zuwa yanzu, kasar ta kashe makudan kudi wajen biyan albashin ‘yan majalisar wakilai da ‘yan majalisar dattawa.

Bayan makudan kudin da Najeriya ta ke kashewa kan ‘yan majalisar tarayya, duk shekara biliyoyi su kan tafi aljihun tsofaffin shugabannin da su ka mulki kasar a shekarun baya.

Najeriya mai samun kudin shiga daga man fetur ta kan ware kaso mai tsoka na musamman ga jihohin Neja-Delta masu ainihin arzikin mai kamar dai yadda tsarin mulki ya tanada.

A shekaru 21 da aka yi ana mulkin farar hula, gwamnatin tarayya ta warewawasu jihohin da ke da mai kudi Naira tiriliyan 8.96%. Daga 1999 zuwa 2019 jihohin su ka samu wannan kudi.

KU KARANTA: An nemi Najeriya an rasa cikin kasashen da su ka yi suna a ilmin boko

Jihohin Bayelsa, Ribas, Delta, Kuros-Riba, Edo, da kuma Abia, Imo, da Ondo su kan samu karin 13% na dukiyar man fetur. Yanzu jihar Legas ta shiga sahun jihohi masu arzikin danyen man.

StatiSense masu tara alkaluma da bincike a Duniya su ka fitar da wannan rahoto. Rahoton ya kuma nuna yadda tsofaffin shugabanni kan tashi da kimanin Naira biliyan 20 duk shekara.

Kusan duk shekara a kan kashe Naira biliyan 2.3 a matsayin alawus din da ake yi biyan tsofaffin shugabannin kasa da mataimakan shugaban kasar a lokacin mulkin soji da na farar hula.

Mafi yawan wadanda su ka yi mulki su na da rai. Shugabannin da su ka mutu kafin 2019 su ne: Tafawa Balewa, Aguiyu Ironsi, Murtala Mohammed, Abacha, da kuma Ummaru ‘Yaradua.

A cewar StatiSense, an batar da Naira tiriliyan 2.75 a kan majalisa ta hudu zuwa majalisa ta tara da ta ke ci a yanzu, wannan ya zarce kasafin kudin Najeriya tun daga 1999 har zuwa 2001.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel