Shugaba Buhari ya maye gurbin mamacin da ya nada a hukumar FCC

Shugaba Buhari ya maye gurbin mamacin da ya nada a hukumar FCC

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya maye gurbin mataccen da ya saka cikin nade-naden hukumar raba daidai ta kasa.

A wata takarda da shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan ya karanta wa majalisar a ranar Talata, 2 ga watan Mayu, shugaban kasar ya ce Daniel James Kolo daga jihar Kwara ya rasu a ranar 19 ga watan Mayu.

Buhari ya bayyana James Gia Kolo a matsayin madadinsa, jaridar The Cable ta ruwaito.

Shugaba Buhari ya maye gurbin mamacin da ya nada a hukumar FCC
Shugaba Buhari ya maye gurbin mamacin da ya nada a hukumar FCC Hoto: The Cable
Asali: UGC

"Don cike tanadin sashi na 154 na kundun tsarin mulkin Najeriya na 1999, ina farin cikin gabatar wa da majalisar da James Gia Kolo a matsayin mamban hukumar daidai ta ayyuka daga jihar Kwara.

"Zai maye gurbin Daniel James Kolo wanda ya rasu a ranar 19 ga watan Mayun 2020," yace.

Wannan ci gaban na tafe ne a kusan makonni uku da shugaban kasar ya maye gurbin Tobias Okwuru, tsohon dan majalisar wakilai, wanda aka zaba a matsayin mamban FCC bayan ya mutu.

Mamacin ya fito ne daga jihar Ebonyi kuma nadin ya kawo tsananin muhawara a kasar nan.

Shugaban kasar ya nada wadanda suka mutu masu tarin yawa da suka rasu a manyan matsayi.

A wata wasika, shugaban kasar ya bukaci majalisar da ta tabbatar da Tella Adeniran a matsayin shugaban hukumar zabe mai zaman kanta na jihar Osun.

KU KARANTA KUMA: Ma su zanga - zanga daga jihar Abia sun mamaye harabar majalisar dattijai

A wani labarin na daban, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya shiga bayan labule tare da shugaban bankin Afrika, Dr Akinwumi Adesina, a fadar shugaban kasa da ke Abuja.

Shugaban kasa Buhari ya karbi bakuncin Mista Adesina tare da shugaban ma'aikatan fadar shugabna kasa, Farfesa Ibrahim Gambari, inda suka shiga ganawa gadan-gadan.

Sauran manyan jami'an gwamntain tarayya da suka gana da Mista Adesina tare da shugaba Buhari sun hadar da Ministar Kudi, Kasafi da tsare-tsaren kasa, Zainab Ahmed.

Sai kuma Ministan harkokin wajen Najeriya, Geoffery Onyeama, mai magana da yawun shugaban kasa, Mista Femi Adesina da sauransu.

AfDB, cibiyar hadin gwiwa ce mallakin kasashen Afirka wadda kasar Amurka ta kasance babbar mai hannun jari a cikinta.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel