Ma su zanga - zanga daga jihar Abia sun mamaye harabar majalisar dattijai

Ma su zanga - zanga daga jihar Abia sun mamaye harabar majalisar dattijai

Masu zanga-zanga a karkashin kungiyar Concerned Citizens of Abia North daga jihar Abia a ranar Talata, sun mamaye majalisar dokokin tarayya.

Sun yi kira ga shugaban majalisar dattawa, Sanata Ahmad Lawan da ya yi gaggawan sanya kujerar bulaliyar masu rinjaye a majalisar, Sanata Orji Uzor Kalu a kasuwa.

Kalu ya kasance dan jam’iyyar All Progressives Congress kuma sanata mai wakiltan yankin Abia ta arewa.

Ma su zanga - zanga daga jihar Abia sun mamaye harabar majalisar dattijai
Ma su zanga - zanga daga jihar Abia sun mamaye harabar majalisar dattijai Hoto: Premium Times
Asali: UGC

A cewar kungiyar, kaddamar da kujerar a kasuwa zai sa hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC) ta gudanar da sabon zabe na wanda zai wakilci Abia ta arewa a majalisar dattawan.

KU KARANTA KUMA: Kisan daliba a coci: Fasto da kungiya mai zaman kanta sun saka kyauta mai tsoka ga wanda ya zo da bayani

Masu zanga-zangar na dauke da kwalayen sanarwa mai rubutu kamar haka:

“Shugaban Majalisar dattawa ka mutunta sashi 68(1)(f) na kundin tsarin mulki sannan ka kaddamar da kujerar sanata mai wakiltan Abia ta arewa a kasuwa; ya zama dole a saurari muryoyinmu, ka sanya kujerar Abia ta arewa a kasuwa yanzun nan.”

Ka kaddamar da kujerar a kasuwa; mazabar Abia ta Arewa na fadin cewa ka kaddamar da kujerar a kasuwa.

A madadin kungiyar, Chukwudi Chuku ya ce, "Mun fito ne daga kananan hukumomi biyar da suka hada da Arochukwu, Bende, Isikwuato, Ohafia da Umunneochi da suka hada mazabar yankin Abia ta arewa.

"Muna kira ga mai girma shugaban majalisar da ya san da cewa bamu da wakilci a majalisar dattawa. Yanke hukunci da daure sanata mai wakiltar mazabar Abia ta arewa, Dr. Orji Uzor Kalu yasa ba a jin muryoyinmu a majalisar.

"Ba mu da wakilci a majalisar dattawan. Muna ji tamkar an manta damu kuma mun fusata don ba a duba mu balle duban abinda zai faru da mu a nan gaba a majalisar.

"A matsayinmu na 'yan kasa masu bin doka kuma muke bin damokaradiyya, muna fatan za ka dubemu tare da duba matsalolinmu ta hanyar bada damar a maye gurbin sanatanmu da wani ta hanyar yin zabe."

A gefe guda mun ji cewa a ranar Talata, 2 ga watan Yuni, wata Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a jihar Legas, ta ba da umarnin sakin tsohon gwamnan jihar Abia, Orji Uzor Kalu, daga kurkuku.

A ranar 5 ga watan Dasumba, 2019, aka yankewa Mista Kalu hukuncin daurin na shekaru 12 a gidan dan Kande.

Hakan ya biyo bayan samunsa da laifin yin ruf da ciki a kan N7.1bn tare da kamfaninsa, Slok Nigeria Limited, da kuma wani tsohon Daraktan Kudi a gwamnatin Jihar Abia, Jones Udeogu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel