Masu zargin ana fada da Musulunci da COVID-19 za su yi tsit yanzu – Ahmad Gumi

Masu zargin ana fada da Musulunci da COVID-19 za su yi tsit yanzu – Ahmad Gumi

A jiya Litinin, 1 ga watan Yuni, 2020, gwamnatin tarayya ta sassauta takunkumin zaman gida a jihar Kano, ta kuma bada damar a bude wuraren ibadar musulmai da kiristoci a fadin kasar.

Fitaccen malamin addinin musulunci, Ahmad Abubakar Mahmud Gumi ya yi magana bayan cire takunkumin, inda ya ce wannan zai kawo karshen mummunan zargin da ake yi wa gwamnati.

Sheikh Ahmad Abubakar Mahmud Gumi ya ce: “Mu na fatar wannan zai rufe bakin masu yi wa gwamnati zargin yunkurin ganin bayan addinin musulunci ta hanyar hana jam’i a masallatai.”

Shehin ya tunawa jama’a cewa a jihar Kaduna mutane sun yi sallar idin su ne a gidajensu, kuma babu abin da hakan ya rage mana inji sa. A karshe aka kuma yi dace babu wanda ya rasu.

“Yanzu da aka sassauta takunkumin kulle a cikin irin wannan yanayi saboda manufar siyasa da tattalin arziki, ya zama dole ga masu ibada su koma sallar jam’i a musunlunci? Ko kusa!”

KU KARANTA: Sheikh Gumi ya yi magana a kan tsige Sanusi II daga sarautar Kano

Babban malamin ya ce sallar jam'i ba ta wajaba a halin da ake ciki na annoba ba. “Muddin annobar ba ta kare ba, kuma akwai yiwuwar kamuwa da cutar, hukuncin zaman gida na nan.”

Ahmad Gumi ya yi wannan rubutu ne a shafinsa na Facebook, ya ce: “Wannan hukunci zai tsaya har zuwa lokacin da kwararrun masana kiwon lafiya su ce an tsira daga kamuwa da cutar.”

Malamin na fikihu ya kara da bada shawarar cewa: “Mutane su yi kokarin gujewa haduwa da juna bakin gwargwado.” Ya ce: “Yara za su iya kamuwa da cutar ba tare da alama ta bayyana ba.”

Haka zalika malamin addinin ya yi kira ga hukuma ta rage kudin hawa shafin yanar gizo domin ba yara damar cigaba da karatunsu ta kafafen zamani a daidai lokacin da makarantu su ke rufe.

“A wannan lokaci ka da mu gaza da addu’o’inmu da taimakon marasa karfi a wannan mawuyacin hali. Allah ya nuna mana karshen wannan lamari cikin koshin lafiya da aminci da imani.”

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng