Rikicin APC: Tinubu ya yi wa gwamnonin APC wa'azin siyasa yayin ganawarsu

Rikicin APC: Tinubu ya yi wa gwamnonin APC wa'azin siyasa yayin ganawarsu

Alamu na nuni da cewa babu gudu, babu ja da baya a batun gudanar da zaben cikin gida domin fidda dan takarar da zai rike kambun jam'iyyar APC a zaben kujerar gwamnan jihar Edo da za a yi a cikin watan Oktoba.

A jiya, Lahadi, ne jagoran jam'iyyar APC na kasa, Asiwaju Bola Tinubu, ya gana da wasu gwamnonin jam'iyyar APC 9 a fadar gwamnatin jihar Legas.

Yayin ganawar tasu, Tinubu ya shaidawa gwamnonin cewa zaben cikin gida na daga cikin ginshikan da ke kara karfafa siyasar cikin gida.

Wata majiya daga cikin taron ta sanar da jaridar 'TheNation' cewa Tinubu ya jaddadawa gwamnonin muhimmancin da ke tattare da gudanar da zaben fidda dan takara tare da yi mu su wa'azin su rike wannan al'adar siyasa mai matukar muhimmanci a tsarin dimokradiyya.

Tun a makon jiya gwamnonin jam'iyyar APC su ka tsara yadda za su matsawa shugaba Buhari lamba domin ya goyi bayan a bar abokansu na jihar Edo da Ondo su sake yin takara ba tare da barin wasu sun yi takara da su a cikin gida ba.

A kalla kimanin mutane 10 ne su ka nuna shawarsu ta neman takarar kujerar gwamnan jihar Ondo a karkashin inuwar jam'iyyar APC.

A jihar Edo, sauran 'yan takarar jam'iyyar APC sun janyewa Fasto Osagie Ize-Iyamu, wanda yake kalubalantar gwamna mai ci, Godwin Obaseki.

An dade ana nuna yatsa tare da musayar maganganu marasa dadi a tsakanin gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki, da shugaban jam'iyyar APC na kasa, Adams Oshiomhole.

Rikicin APC: Tinubu ya yi wa gwamnonin APC wa'azin siyasa yayin ganawarsu
Tinubu da gwamnonin APC
Asali: Twitter

Rahotanni sun bayyana cewa Obaseki ya shiga damuwa bayan ya fahimci cewar Oshiomhole na shirya ma sa tuggun da zai iya jawo ma sa rasa kujerarsa a zaben fidda dan takarar gwamna na jihar Edo wanda za a yi a cikin watan Yuni.

DUBA WANNAN: Salon nadin mukamanka zai tarwatsa Najeriya - Kanal Dangiwa Umar ya rubutawa Buhari wasika

An samu sabanin ra'ayi a kan hanyar da za a gudanar da zaben fidda dan takara a tsakanin bangaren gwamna Obaseki da bangaren uwar jam'iyyar APC a karkashin jagorancin Oshiomhole.

A yayin da gwamna Obaseki ke son a yi amfani da wakilan jam'iyya domin gudanar da zaben, bangaren Oshiomhole sun kafe a kan a yi kato bayan kato.

Tinubu ya ce ya goyi bayan a gudanar da zaben fidda 'yan takara a cikin jam'iyya domin yin hakan shine tsarin dimokradiyya ta gaskiya da adalci, kuma ta hakan ne kawai dan takara zai gwada karbuwa da farin jininsa a wurin jama'a, wanda hakan shine al'adar siyasa.

Rahotannin sun bayyana cewa Tinubu ya nemi a yi wa gwamnonin da ke kan mulki da sauran ma su sha'awar takara adalci a yayin da ya ke jaddada cewa gudanar da zaben cikin gida zai kara karfafa dimokradiyya da bawa dan takara karfin gwuiwa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel