Sojoji sun yi fada da ‘Yan Sanda bayan an ci wani jami’i tarar N10, 000

Sojoji sun yi fada da ‘Yan Sanda bayan an ci wani jami’i tarar N10, 000

Wani karamin rikici ya barke da ranar yau Litinin dinnan tsakanin wasu jami’an sojoji da kuma ‘yan sanda a karamar hukumar Zariya, a jihar Kaduna.

Rigimar ta kaure ne yayin da jami’an ‘yan sanda su ka ci tarar wani Soja da aka samu ya na yawo a gari a lokacin da ake cikin takunkumin zaman gida.

Rahotanni sun bayyana cewa wannan soja ya na dauke ne da kayan zaman gida a lokacin da ya fada hannun ‘yan sanda da sunan sabawa dokar kulle.

Jaridar Daily Trust ta ce an yankewa wannan jami’in tsaro tarar N10, 000 a kotun wucin-gadi da aka kirkira domin takaita zirga-zirga saboda COVID-19.

Yayin da wannan soja ya ke neman ‘yan sanda su yi masa bayanin abin da ya sa aka ci shi tara kenan sai wani jami’in ‘yan sanda ya datsa masa mari.

Wani wanda abin ya faru a idonsa ya shaidawa jaridar cewa nan take fada ya kaure tsakanin jami’an tsaron bayan an shararawa wannan soja mari.

KU KARANTA: Tsohon Saurayi ya na neman Matar Hameed Ali ta biya shi N9m

Sojojin da ke wurin sun marawa abokin aikinsu baya, yayin da alkalin da ke hukunci a wannan kotu ya tsere da ya ga yadda abin ya kasance a kotun.

Da aka tuntubi mataimakin darektan yada labarai na barikin sojoji game da takaddamar, Kyaftin Audu Arigu ya ce an shawo kan sabanin da aka samu.

Arigu ya shaidawa manema labarai dazu cewa ‘yan sandan da sojojin duk sun hallara a babban barikin na Zariya, inda aka samu sulhunta tsakaninsu.

Legit.ng Hausa ta samu labarin cewa an fara wannan rikici ne da kimanin karfe 1:00 na rana a daidai hanyar agoro da ke cikin unguwar Tudun Wada.

Mun ga motocin ‘yan sanda su na ta faman shawagi a daidai wani gidan mai bayan rigimar ta kaure. Kawo yanzu mun ji cewa abubuwa sun lafa a Garin.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel