Wani tsohon Saurayi ya bukaci Matar Hameed Ali ta biya shi miliyoyin kudi

Wani tsohon Saurayi ya bukaci Matar Hameed Ali ta biya shi miliyoyin kudi

Wani Bawan Allah, Zubairu Dalhatu Malami ya dauki hayar lauyoyi ya na neman Zainab Yahaya wanda ya yi ikirarin tsohuwar masoyiyarsa ce, ta biya sa wasu makudan kudi.

Zubairu Dalhatu Malami ya rubuta takarda ta hannun lauyoyinsa ga Zainab Abdullahi Yahaya, amaryar shugaban hukumar kula da fasa kauri a Najeriya watau Kanal Hameed Ali.

Kwanaki kadan da yin auren Ali wanda ya rasa mai dakinsa a 2018, sai takarda ta fito wanda aka rubuta a ranar 22 ga watan Mayu, ana neman amaryar ta biya Naira miliyan tara.

Zubairu Dalhatu ya ce ya kashewa wannan mata kudi fiye da Naira miliyan tara da dubu 80 a lokacin da su ke zabga soyayya, sai kuma daga baya ta lallaba ta auri wani dabam.

Wannan mutumi ya yi wa mai dakin shugaban gidan kwastam lissafin duk irin kudin da ya kashe a kanta, da kuma bashi da jari da ya bata a tsawon shekaru uku da su ka yi.

KU KARANTA: Hameed Ali ya zama Ango, ya sake aure bayan rasuwar mai dakinsa

A cewar Zubairu Dalhatu, har kayan lefe ya saya, amma daga baya Zainab ta tsere ta bar shi. Wannan mutumi ya bukaci amaryar ta fito masa da duk kayansa da ke hannunta.

Daga cikin kudin da Zubairu ya ce ya kashe akwai jarin wasu kaya daga Amurka na N450, 000. N2, 778, 207. 48 zuwa kasashen Saudi da Dubai da Sin da aron jarin N1, 500, 000.

Haka zalika ya ce ya ba ta N280, 000 domin ta kama wani shago a birnin Kano, sannan da wasu N350,000 da ta ba mahaifinta. Har ila yau ya ce ta karbi kudin haya na N350, 000.

Zubairu ya na ikirarin kashe N1.7m a kan lefe, N300, 000 wajen sayen lullubai, da wasu N360, 000 wajen keta hazo zuwa kasar Sin. Haka zalika ya bata N500, 000 domin ta saye mota.

Takardar lauyoyin sun nuna cewa har da wasu N250, 000 wannan Bawan Allah ya kashewa tsohuwar sahibarsa domin ta fara sana’ar cin-cin. Jimillar kudin sun haura miliyan 9.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel